Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

Gwamnatin Ebonyi ta sanar da bawa jami'an tsaro amfani da matsaikacin horo a kan jama'a a matsayin matakin dakile yaduwar annobar cutar covid-19 a jihar.

Duk da har yanzu ba a samu rahoton bullar annobar cutar covid-19 a Ebonyi ba, gwamnan jihar, David Umahi, ya ce akwai bukatar daukan tsauraran matakai domin ganin ba ta samu hanyar shigowa jihar ba.

Da ya ke gabatar da jawabi ranar Laraba, Umahi ya ce an bawa jami'ai umarnin yin bulala ga duk wanda ya fita daga gida ba tare da takunkumi ba.

Umahi ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar a gaban ma su ruwa da tsaki a yaki da annobar cutar covid-19 a fadar gwamnatin jihar Ebonyi da ke Abakaliki.

Ya ce, "bari na sake yin gargadi; babu wanda zai motsa a Ebonyi ba tare da takunkumin fuska ba.

"Na bawa jami'ai izinin yin amfani da matsaikacin horo a kan duk wanda aka samu ya saba dokar amfani da takunkumin fuska, hakan ya hada da yin bulala ga ma su kunnen kashi," a cewarsa.

Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

David Umahi
Source: Twitter

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya saka dokar amfani da takunkumi ga duk dan jihar Kaduna da fita waje ta kama dole.

Gwamnan ya saka dokar ne a cikin jawabinsa na farko da ya fitar bayan warkewarsa daga cutar covid-19.

DUBA WANNAN: Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano albarkacin watan Ramadana

A jiya, Laraba, ne rahotanni su ka bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya warke daga cutar coronavirus.

El-Rufa'i ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (tuwita) cewa ya warke daga cutar covid-19 bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa iyalinsa sun shiga cikin matsananciyar damuwa yayin da sakamakon gwaji ya nuna cewa ya na dauke da kwayar cutar.

A cewar El-Rufa'i, bayan an killace shi na kusan sati hudu, sakamakon gwajin kwayar cutar da aka sake yi ma sa har sau biyu ya nuna cewa yanzu ya rabu da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel