Yanzu-Yanzu: Covid-19 ta hallaka mutane 2 a Legas

Yanzu-Yanzu: Covid-19 ta hallaka mutane 2 a Legas

An sake samun mutuwar wasu mutane biyu a jihar Legas a sanadiyar cutar Coronavirus.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, shi ne ya tabbatar da wannan rahoto da ya wallafa a kan shafinsa na sada zumunta a ranar Alhamis.

Farfesa Abayomi ya ce a ranar Laraba an sake samun sabbin mutane 74 wanda cutar corona ta harba, inda jimillar masu dauke da cutar ya kai 512 a jihar.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Abayomi ya ce "an samu karin mutane 74 wanda cutar coronavirus ta harba a jihar a ranar Laraba, 22 ga Afrilu, 2020."

"Jimillar masu dauke da cutar a jihar sun kai 512."

"Jimillar wadanda cutar Coronavirus ta hallaka a jihar sun kai 18."

KARANTA KUMA: Gwamnatin Lebanon ta nuna bacin rai kan dan kasarta da ke neman sayar da wata 'yar Najeriya

A yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da aiki tukuru babu dare babu rana domin hana yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, cutar tamkar wutar daji na ci gaba da bazuwa a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 26 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taswirar NCDC a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 873 a Najeriya yayin da tuni mutane 197 suka warke daga cutar.

Ya zuwa yanzu dai mutane 28 cutar ta hallaka a duk fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Babu shakka jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutane da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu.

Taskar bayanai ta Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar cewa jimillar mutane da cutar ta harba a fadin duniya ta kai 2,639,243 yayin da mutane 183,820 suka riga mu gidan gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel