COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki

COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki

- Kwamitin shugaban kasa na yakar cutar Covid-19 ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali

- Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a jiya yayin jawabi ga kwamitin

- Ya mika godiyarsa ga sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a kasar nan a kan kwamitin fatawa ta gaggawa da ya kafa

Kwamitin shugaban kasa na yakar cutar Covid-19 ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a jiya yayin jawabi ga kwamitin.

Ya ce: "Halin da jihar Kano ke ciki abin tada hankali ne. Kwamitin na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don shawo kan lamarin.

"Kwamitin ya gano cewa ana ci gaba da samun masu cutar a kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da yadda aka fadada wuraren gwajin."

Mustapha ya kara da cewa, ganin yadda lamarin ya sake yawaita, sun sauya sabbin tsarin gwaji don yanzu gida-gida ake bi don yin gwajin a jihohin Legas da Abuja.

Kamar yadda yace, gwaji, tantancewa, killacewa da kula da masu cutar ya zama dole in har ana bukatar takaita yawan masu kamuwa da cutar.

Ya mika godiyarsa ga sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a kasar nan a kan kwamitin fatawa ta gaggawa da ya kafa.

COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki
COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki
Asali: Facebook

KU KARANTA: Covid-19: Yadda dandazon jama'a ke hada-hada a kasuwannin FCT

Ta hakan ne aka samu wadanda suka wayar da kai ga al'umma ta yadda za a yi azumin watan Ramadan duk da dokar.

A yayin martani ga rahoton daraktan bangaren binciken cututtuka masu yaduwa na asibitin koyarwa na Aminu Kano, Farfesa Isah Abubakar, ministan ya ce an shawo kan matsalar.

Ya bayyana cewa an kai sinadaran gwajin duk da sun kare amma kuma wasu daga cikin masu aiki a dakin gwajin ne suka samu cutar.

Don haka aka dakatar da aiki a wurin har sai an yi masa feshi.

"Na wucin-gadi ne aka dakatar da yin gwajin amma yanzu an samar da sinadaran tare da kayan bada kariya ga ma'aikatan yayin da suke aiki," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel