Karanta wasu alkalumma masu rikitarwa game da annobar Coronavirus

Karanta wasu alkalumma masu rikitarwa game da annobar Coronavirus

Majalisar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta bayyana zuwa yanzu, annobar Coronavirus ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a duniya gaba daya.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreysus ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru game da annobar a ranar Laraba a birnin Geneva, kasar Switzerland.

KU KARANTA: Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

“A duniya gaba daya, mutane miliyan 2.5 ne cutar COVID-19 ta kama, kuma an samu mace mace 160,000 a dalilin ta.” Inji shugaban WHO, Tedros Ghebreysus.

Tedros Ghebreysus ya ce an samu bambancin yaduwa da barnar da ta yi a kasashe da nahiyoyin duniya daban daban, inda yace a yanzu annobar ta fara lafawa a yammacin nahiyar turai.

“Da yake ana samun saukin annobar a yanzu a yammacin nahiyar turai, amma muna tsoron yadda yake tashi a nahiyar Afirka, tsakiyar Amurka, kudancin Amurka da kuma gabashin turai, yawancin kasashen yankunan nan yanzu suke fara fuskantar matsalar.

“Yayin wadanda suka fuskanci matsalar annobar a baya, suna sake samun farfadowarta, maganar gaskiya akwai sauran aiki a gabanmu, wannan annobar za ta dade tare da mu bata tafi ba.” Inji shi.

Karanta wasu alkalumma masu rikitarwa game da annobar Coronavirus

Karanta wasu alkalumma masu rikitarwa game da annobar Coronavirus
Source: UGC

Tedros Ghebreysus yace dokar zaman gidan da gwamnatocin kasashen duniya suka sanya ya taimaka wajen takaita yaduwar cutar, amma duk da haka cutar nan abin tsoro ce.

Daga karshe Tedros Ghebreysus ya ce har yanzu al’ummar duniya suna cikin hadari saboda cutar ka iya farfadowa tare da cigaba da yaduwa a duniya.

“Babbar matsalar da muke fama da ita a yanzu shi ne kasashe suna yin sakwa-sakwa game da dokar zaman gida da takaita zirga zirga saboda jama’a sun fara gajiya da zaman gida.”

A wani labari kuma, Gwamnan jahar Oyo ya sanar da samun mutuwar mutum na farko sakamakon annobar Coronavirus da ta kama shi a jahar, a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu.

Gwamna Seyi Makinde ya bayyana haka ne da misalin karfe 11:30 na daren Laraba a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel