Gwamnatin Lebanon ta nuna bacin rai kan dan kasarta da ke neman sayar da wata 'yar Najeriya

Gwamnatin Lebanon ta nuna bacin rai kan dan kasarta da ke neman sayar da wata 'yar Najeriya

Gwamnatin Lebanon ta yi martani kan wani dan kasarta mai suna Wael Jerro, wanda a ranar Talata ya tallata hoton wata mata 'yar Najeriya a shafin Facebook yana neman mai saya.

Jerro wanda mazaunin birnin Beirut ne a kasar Lebanon, ya tallata hoton matar mai shekaru 30 tare da duk wasu bayananta a shafin wata kungiya a dandalin sada zumuntar mai lakabin ‘Buy and Sell Lebanon.’

Ya sanya farashin matar da ya misalta a matsayin 'yar aikin gida a kan dalar Amurka 1000, da cewar 'yar Najeriya tana da kwazo wurin aiki kuma ga tsabta.

Da ta ke bayyana bacin ranta, gwamnatin Lebanon ta bayyana lamarin a matsayin haramtacce kuma mafi kololuwar rashin hankali da mugunta.

Sai dai gwamnatin ta sha alwashin daukar matakin gaske a kan Jerro kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A Yammacin Laraba ne babbar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri Erewa, ta yi karin haske a kan lamarin.

Mrs Dabiri a shafinta na zauren sada zumunta ta wallafa bacin ran gwamnatin kasar Lebanon, tare da bayyana matakin da za ta dauka kan dan kasarta.

KARANTA KUMA: Za a fara gwajin riga-kafin cutar korona a Jamus

Hadimar shugaban kasar ita ce ta shigar da korafin wannan lamari zuwa ga hukumomin kasar Lebanon, inda kuma suka waiwayeta cikin gaggawa.

'Yan Najeriya da dama mabiya shafin Twitter, sun bayyana fushin su dangane da wannan tsangwama da suka misalta a matsayin mafi kololuwar cin mutuncin dan Adam.

A na iya tuna cewa a makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta gargadi hukumomin kasar China kan tsangwamar 'yan kasar ta da ake yi mazauna can.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana nuna wa bakaken fata wariyar launi a kasar China bisa zargin cewa su na dauke da cutar Coronavirus.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, ya nuna bacin rai kwarai da gaske dangane da irin wulakantaswa da ake yiwa 'yan Najeriya a kasar China saboda cutar corona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel