Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 91 sun kamu da Coronavirus yau

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 91 sun kamu da Coronavirus yau

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 91 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Laraba, 22 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane dari da sha bakwai (17) sun kamu da #COVID19"

74 a Lagos

5 a Katsina

4 a Ogun

2 a Delta

2 a Edo

1 a Kwara

1 a Oyo

1 a FCT

1 a Adamawa

Kawo karfe 11:25 na daren 22 ga Afrilu, mutane 873 suka kamu da COVID-19 a Najeriya.

An Sallami: 197

Mutuwa: 28

KU KARANTA: Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano

Gajerin jihohin Najeriya da adadin wadanda suka kamu

Lagos-504, FCT-119, Kano-73, Ogun-24, Katsina-21, Osun-20 Oyo-17, Edo-17, Kwara-10. Kaduna-9, Akwa Ibom-9, Borno-9, Bauchi-8, Delta-6, Gombe-5, Ekiti-4, Ondo-3, Rivers-3, Jigawa-2, Enugu-2 Niger-2, Abia-2, Benue-1, Anambra-1, Sokoto-1, Adamawa-1

A bangare guda, dukkan gwamonin jihohin Najeriya 36 su ka amince da kaddamar da dokar kulle kasa baki daya har na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19.

Gwamnonin, a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), sun cimma wannan matsaya ne bayan sauraron bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun a kan darussan da su ka koya daga yaki da annobar covid-19.

Shugaban kungiyar NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ne ya fitar da wannan sanarwa bayan kammala taron gwamnonin da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel