Sai da lambar BVN za ku samu albashinku na wata biyu - FG ta gargadi ASUU

Sai da lambar BVN za ku samu albashinku na wata biyu - FG ta gargadi ASUU

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta lashi takobin cigaba da rikewa mambobin kungiyar malaman jami'a ASUU da suka yiwa gwamnati bore ba muddin suka ki bada lambar BVN dinsu.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne yayin hirar kwamitin kar ta kwana na yakin da COVID-19 ta kasa da manema labarai a Abuja.

A cewarsa, tausayi shugaba Buhari ya ji ya bada umurnin a biyasu kudin albashinsu da aka rike amma sai shugabannnin jami'a sun amshi lambobin BVN dinsu za'a iya biya.

Yace: "Amma, sai dukkan shugabannin jami'o'i sun tattara lambobin BVN na malaman kafin akawunta janar zai iya biya."

A nasu bangaren kuwa, shugaban kungiyar Malaman jami'o'in ASUU, Biodun Ogunyemi, ya yi kira ga lakcarorin kada su sake su bada lambar BVN dinsu.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba a Abuja inda yace: "Mun godewa shugaban kasa da yin haka amma ai tun farko bai kamata ma ya rike mana albashin Febraairu da Maris ba."

"Abu na biyu, mambobinmu basu amince da sharadin cewa sai mun bada lambobin BVN kafin a biyamu ba."

"Saboda muna tunanin ana kokarin sanyamu cikin shirin IPPIS ne ta bayan fagge,"

IPPIS dai wata manhaja ce ta bau daya na biyan albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya wacce zata saukake gano ma'aikatan bogi a gwamnati.

Sai da lambar BVN za ku samu albashinku na wata biyu - FG ta gargadi ASUU

Sai da lambar BVN za ku samu albashinku na wata biyu - FG ta gargadi ASUU
Source: UGC

A ranar Talata, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin biyan albashin lakcarorin jami'a da suka yiwa gwamnati bore ta hanyar kin rijista kan manhajar IPPIS.

Shugaban kasan ya ce a biyasu ne bayan ganawar da yayi da ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, jiya a Abuja.

Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya sun dade da shiga takun tsaka kan lamarin rijista kan manhajar biyan albashi na zamani wato IPPIS.

Minista Ngige ya bayyanawa manema labarai cewa shugaba Buhari ya umurci ministar kudi, Zainab Shamsuna, da akawunta janar na tarayya, Ahmed Idris, suyi gaggawan biyan lakcarorin.

Buhari ya ce a biyasu ne saboda irin halin kuncin da zasu iya shiga sakamakon rashin albashin watanni biyu cikin halin zaman gida da annobar Coronavirus ta sabbaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel