Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

A kokarin ta na rage ma talakawa radadin mawuyacin halin da ake ciki sakamakon annobar Coronavirus, kungiyar matan hafsoshin rundunar Sojan sama, NAFOWA ta yi rabon tallafi.

NAFOWA ta yi rabon kayan ne domin bikin cikar rundunar Sojan sama shekara 56 da kirkira, don haka ta yi amfani da wannan dama domin faranta ma jama’a marasa galihu.

KU KARANTA: Wata babbar Coci ta raba ma Musulmai 300 kayan abincin azumi a jahar Kaduna

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja
Source: Facebook

NAFOWA ta yi rabon ne a garin Bassa, Sauka da Wulumo dake babban birnin tarayya Abuja, inda ta raba ma iyalai 550 buhunan shinkafa, man gyada, wake, indomie, Semovita da sauransu.

A jawabin ta yayin kaddamar da rabon, shugabar NAFOWA, Hajiya Hafsat Abubakar, wanda ta samu wakilcin mataimakiyarta, Elizabeth Amao ta ce sun yi haka ne don jin kan talakawa.

Amao ta kara da cewa fatansu tallafin zai rage ma wadanda suka amfana radadin halin da ake ciki, kuma ta nemi su cigaba da bin ka’idojin da aka shimfida don yaki da cutar COVID-19.

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja
Source: Facebook

A jawabin sa, shugaban al’ummar Bassa, Gimbia Daudu ya ce tun bayan da aka garkame Abuja, jama’ansa basa iya samun abinci, don haka yace wannan tallafin zai taimaka sosai.

Su ma sauran jama’an da suka ci gajiyar tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da mika godiyar su da sakon jinjina ga kungiyar NAFOWA, suka yi fatan Allah Ya saka musu da alheri.

A hannu guda, gwamnan jahar Gombe, Inuwa Yahaya ya sanya dokar hana shige da fice a fadin jahar daga karfe 6 na dare zuwa 7 na safe, har sai yadda hali yayi.

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, inda yace ya dauki wannan mataki ne don kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Cikin sanarwar da ya fitar, Gwamna Yahaya ya ce dokar hana shige da ficen zai fara aiki ne daga karfe 6 na yammacin Alhamis, don haka ya nemi jama’an jahar su yi zaman su a gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel