Wata babbar Coci ta raba ma Musulmai 300 kayan abincin azumi a jahar Kaduna

Wata babbar Coci ta raba ma Musulmai 300 kayan abincin azumi a jahar Kaduna

Cocin Christ Evangelical Intercessory and Life Intervention Ministry dake unguwar Sabon Tasha, a Kaduna ta raba ma al’ummar Musulmai kayan abinci da na masarufi.

Daily Nigerian ta ruwaito Cocin ta raba ma Musulmai 300 kayan abinci ne a sakamakon karatowar azumin watan Ramadana a unguwar Rigasa, cikin karamar hukumar Igabi.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi

Cocin sun yi rabon ne a ranar Laraba a karkashin jagorancin babban faston Cocin, Yohanna Buru wanda yace akwai bukatar su taimaka ma Musulmai duba da azumi na karatowa.

Bugu da kari, Yohanna Buru yace tallafin zai rage ma Musulmai radadin mawuyacin halin da ake ciki sanadiyyar dokar hana fita saboda Coronavirus, musamman a watan Ramadan.

Wata babbar Coci ta raba ma Musulmai 300 kayan abincin azumi a jahar Kaduna
Yayin rabon
Asali: Facebook

“Wannan ne karo na biyar da cocinmu ta raba buhunan hatsi da sauran kayan abinci ga mabarata, yan gudun hijira, gidajen marayu da kuma Musulmai dake zaune a gidajen yari a fadin jahar.

“A bara, mun raba buhunan hatsi da kayan abinci ga talakawa Musulmai a jahohi 5 domin su samu daman yin walwala a yayin watan azumin Ramadana tare da yin ibada cikin kwanciyar hankali.

“A wannan karo mun hada da tabarmai da butocin alwala ta yadda zasu gudanar da ibadojinsu cikin kwanciyar hankali daga gidajensu, tare da gabatar da addu’o’i ga Allah don Ya kawo mana dauki game da wannan bala’i da ake ciki.” Inji shi.

Buru ya ce, wannan taimako da suka bayar, wata hanya ce ta kara karfafa dankon zumunci da zaman lafiya tsakanin mabanbanta addinai a Kaduna kamar yadda addininsu ya koyar dasu.

Daga karshe ya yi kira ga masu hannu da shuni su shiga a dama dasu wajen taimaka ma al’umma domin rage musu radadin halin da suke ciki, musamman ga talakawa da gajiyayyu.

Faston bai tsaya nan ba sai da ya gargadi yan kasuwa da su ji tsoron Allah su daina tsawwala farashin kaya a wata mai albarka watan Azumin Ramadan don neman kazamar riba.

Ya kara da cewa sun fara shirin kai ziyara kasuwanni kamar yadda suka saba don jan hankalin yan kasuwan tare da neman su rangwanta farashi ga jama’a a Ramadan.

Da take amsan kayan, shugaban mata masu bukata na musamman a yankin Rigasa, Jummai Muhammad ta bayyana farin cikinta da alherin da cocin ta musu.

“Za’a fara azumi, amma ba mu da ko abincin ci a gidanmu, dole ta sa muke fita bara, annobar Coronavirus ta addabe mu, ta sa farashin kayan abinci ya tashi sosai, don haka mun gode ma yan uwan Kiristoci da suka kawo mana tallafi.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel