'Ka ceci jihar Kano' - Sanata Barau Jibrin ya roki Buhari

'Ka ceci jihar Kano' - Sanata Barau Jibrin ya roki Buhari

Shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin, ya roki gwamnatin tarayya ta taimakawa jihar Kano da kudi domin ta shawo kan annobar cutar covid-19.

Sanata Jibrin, mamba mai wakiltar sanatoriyar Kano ta arewa a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

A cikin jawabin da ya fitar, wanda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa, sanata Barau ya ce gwamnatin jihar Kano ta na bukatar kudi, kayan aiki da karin cibiyoyin gwaji.

A cewar dan majalisar, jihar Kano ta cancanta ta samu tallafi mai tsoka daga gwamnatin tarayya, saboda ita ce jiha mafi yawan jama'a Najeriya.

Sanata Jibrin ya bayyana cewa tallafawa Kano tamkar bawa arewacin Najeriya da ma kasa baki daya tallafi ne, saboda muhimmancin da jihar keda shi a kasa.

Dan majalisar ya roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taimakwa Kano domin ta shawo kan annobar cutar covid-19 da ke yi wa jihar barazana a halin yanzu.

'Ka ceci jihar Kano' - Sanata Barau Jibrin ya roki Buhari
Sanata Barau Jibrin
Asali: UGC

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bawa Legas tallafi wajen yaki da annobar cutar covid-19 saboda muhimmancin jihar ga kasa.

Ya roki gwamnatin tarayya da kar ta tsaya jiran sai annobar covid-19 ta fi karfin gwamnatin jihar Kano kafin ta bayar da tallafinta.

DUBA WANNAN: Yadda launin fatar wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19 (Hoto)

Sanata Jibrin ya jinjinawa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa daukan matakan gaggawa domin dakile annobar covid-19 a Kano.

Ya bayyana cewa hatta shugaban hukumar shawo kan cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu, ya yi jinjina tare da yabawa kokarin gwamna Ganduje yayin ziyarar da ya kai jihar.

"Babu wata jiha a Najeriya da za ta iya yaki da annobar covid-19 ba tare da tallafin gwamnatin tarayya ba.

"Ina rokon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gaggauta taimakawa jihar Kano a wannan lokaci," a cewar sanata Barau.

Kazalika, ya bayyana cewa alkaluma sun nuna cewa a halin yanzu jihar Kano ce a mataki na uku; bayan Lagos da Abuja, a yawan ma su dauke da kwayar cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel