Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku

Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku

- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya bada shawarar yadda za a bada kariya ga tattalin arzikin kasar nan

- Kamar yadda Atiku ya bayyana, akwai bukatar Najeriya ta samu ma'adanar danyen man fetur din don gudun siyar da shi a yayin da kasuwarsa tayi warwas

- Atiku ya kara da bayyana cewa, Amurka ta Arewa da kasashen Turai duk suna da hanyoyin da suke bi don bada kariya ga dukkan bangarori na tattalin arzikinsu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bada shawarar yadda za a daidaita tattalin arzikin kasar nan duk da annobar da ta addabi duniya.

Kamar yadda ya bayyana, "Kasuwar man fetur ta duniya na ci gaba da samun koma baya sakamakon annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

"Ana ci gaba da samun tabarbarewar farashin man fetur din a duk fadin duniya.

"Haka kasuwa ta gada, wata rana tayi kyau inda wata rana kuwa ta fadi warwas. A yau annobar Covid-19 ce sanadi, wata rana kuwa wani abu ne daban.

"Lokaci ya yi da za a samar da kariya mai dorewa ga tattalin arzikin kasar nan gudun ya dinga sama da kasa har a gagara iya juya shi."

Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku

Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

Jaridar The Nation Online ta ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, "Na sakankance cewa yanzu lokaci ya yi da Najeriya za ta kafa ma'adanar danyen man fetur mai matukar rinjaye a duniya.

"Idan muka gina ma'adanar man fetur din, ba za mu siyar da shi a yayin da ya fadi warwas ba. Za mu yi ta adana shi har sai lokacin da farashin ya daidaita.

"Hakan ne ya kamata kasar nan ta fara yi don bada kariya ga tattalin arzikinta.

"Amurka ta Arewa da kasashen Turai duk suna da hanyoyin da suke bi don bada kariya ga dukkan bangarori na tattalin arzikinsu.

"Bai kamata a bar Najeriya a baya ba, dole ne mu shiga wannan lamarin don bada kariya ga tattalin arzikin kasar nan."

Ya sake shawartar gwamnati da cewa, "Ina kara bada shawarar cewa mu tattauna da abokanmu ta bangaren kasashe masu fitar da danyen man fetur don samun matsaya.

"A hakan ne kadai za mu iya shawo kan matsalar faduwar farashin man fetur don samun daidaito a tattalin arzikin kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel