COVID-19: Gwamnatin Kano ta mayar da Almajirai 419 zuwa Katsina

COVID-19: Gwamnatin Kano ta mayar da Almajirai 419 zuwa Katsina

Almajirai guda 419 ne gwamnatin jihar Katsina ta karba daga hannun gwamnatin jihar Kano da aka bukaci su koma jihohinsu na haihuwa a yunkurin Kano ke yi na takaita yaduwar Covid-19.

Direktan watsa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina, SGS, Alhaji Abdullahi Yar’adua ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya raba wa menama labarai a ranar Laraba a Katsina.

Sanarwar ta jadadda cewa SSG, Alhaji Mustapha Inuwa ya karbi almajiran ne a madadin gwamnatin jihar Katsina kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa an jiyo inuwa yana bayyana farin cikinsa kan yadda jihohin Katsina da Kano ke daukan matakai iri daya domin takaita yaduwa cutar da coronavirus a jihohinsu.

COVID-19: Gwamnatin Kano ta mayar da Amajirai 419 zuwa Katsina
COVID-19: Gwamnatin Kano ta mayar da Amajirai 419 zuwa Katsina
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnonin Arewa sun amince da haramta Almajiranci a yankin

Ya yi bayyanin cewa tuni gwamnatin jihar ta rufe makarantun islamiyya da na allo, ta kuma mayar da almajirai gidajen iyayen su har da wadanda suka zo daga Jamhuriyar Nijar.

Ya mika godiyarsa ga gwamnatin Kano kan yadda ta tantance yaran sannan ta killace su kafin ta mika su ga jihar su.

SGS din ya sanar da cewa za a bawa dukkan yaran masauki sansanin bai wa masu yi wa kasa hidima a Katsina domin a sake duba lafiyarsu kafin a kai su gidajen iyayensu a kananan hukumomin jihar.

Ya gargadi iyaye su guji aike wa da yaransu zuwa wuraren da ba su sani ba da ka iya jefa rayuwarsu cikin hatsari da sunan neman ilimin addini.

A cewarsa, hakkin iyaye ne su kula da yaransu su kuma basu tarbiya wanda a halin yanzu ba a samun hakan idan an tura su almajiranci.

Sanarwar ta kuma ce Kwamishinan Ilimi na Kano, Alhaji Muhammad Majidadin-Kiru ya yaba da kokarin gwamnatin na Katsina yayin da ya ke mika yaran a kan iyakar Kano da Katsina kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel