Yanzu-yanzu: Bayan kimanin wata daya, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Bayan kimanin wata daya, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya warke daga Coronavirus

Bayan kimanin makonni hudu da kamuwa da muguwar cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus, gwamnan jihar Kaduna , Nasir El-Rufai, ya samu waraka.

Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ranar Laraba, 22 ga Afrilu, 2020.

Yace “Ina farin cikin sanar muku a yau cewa bayan kimanin makonni hudu na jinya mai tsanani, na samu labarin sakamakon gwaji biyu daban-daban na cewa na warke daga cutar.“

“Ina mika godiya ga Allah madaukaki bisa niimansa da rahamansa. Hakazalika ina mika godiya ga alumma bisa tausayinsu da addu'o'insu lokacin da suka samu labarin rashin lafiyata.“

“Iyalaina sun ji matukar tsoron yiwuwan rasa ni da kuma tsoron kamuwa da cutar. Dukkan iyalaina sun bani hadin kai, yayinda abokan arziki daga fadin duniya suka aiko da addu'o'insu.“

“Ina godewa likitocinmu na maaikatar kiwon lafiyarmu da asibitin koyarwan Barau Dikko da sukayi bajinta bisa iyawan da suka nuna.“

Yanzu-yanzu: Bayan kimanin wata daya, gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya warke daga Coronavirus

Nasir El-Rufai, ya warke daga Coronavirus
Source: Facebook

El-Rufai shine gwamna na uku da ya kamu da cutar Coronavirus a Najeriya kuma ya samu sauki bayan jinya.

Sauran takwaransa da suka fuskanci irin haka sune gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed.

El-Rufai ne wanda yafi dadewa cikinsu yana jinya.

A wani labarin daban, An yi zargin cewa tsoron kamuwa da cutar coronavirus ya sanya wasu likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar Enugu sun bari wata mata ta riga mu gidan gaskiya.

Fargabar kamuwa da annobar corona wadda ta zama ruwan dare ta sanya wasu likitoci sun haifar da mutuwar wata mata uwar 'ya'ya hudu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, matar mai shekaru 35 ta riga mu gidan gaskiya bayan da likitoci sun kauracewa duban lafiyar ta domin gudun kamuwa da cutar corona.

Mijin wannan mata, Nwachukwu Alagbu mai shekaru 40 a duniya, ya bayyana damuwa kwarai da gaske dangane da sakacin da ma'aikatan lafiya suka yi wajen ceto ran mai dakinsa.

Mista Alagbu ya ce sakacin likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na asibiti ne yayi sanadiyar mutuwar matarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel