IPPIS: Buhari ya dagawa Lakcarorin Jami'a kafa, ya ce a biyasu albashin watanni 2 da ya rike

IPPIS: Buhari ya dagawa Lakcarorin Jami'a kafa, ya ce a biyasu albashin watanni 2 da ya rike

Bayan watanni biyu babu albashi, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin biyan albashin lakcarorin jami'a da suka yiwa gwamnati bore ta hanyar kin rijista kan manhajar IPPIS.

Shugaban kasan ya ce a biyasu ne bayan ganawar da yayi da ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, jiya a Abuja.

Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya sun dade da shiga takun tsaka kan lamarin rijista kan manhajar biyan albashi na zamani wato IPPIS.

Minista Ngige ya bayyanawa manema labarai cewa shugaba Buhari ya umurci ministar kudi, Zainab Shamsuna, da akawunta janar na tarayya, Ahmed Idris, suyi gaggawan biyan lakcarorin.

Buhari ya ce a biyasu ne saboda irin halin kuncin da zasu iya shiga sakamakon rashin albashin watanni biyu cikin halin zaman gida da annobar Coronavirus ta sabbaba.

IPPIS: Buhari ya dagawa Lakcarorin Jami'a, ya ce a biyasu albashin watanni 2 da ya rike

IPPIS: Buhari ya dagawa Lakcarorin Jami'a, ya ce a biyasu albashin watanni 2 da ya rike
Source: UGC

KU KARANTA Dan gwagwarmaya IG Wala ya samu afuwar shugaban kasa, ya shaki iskar 'yanci

Sanata Ngige yace, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau ya bada umurnin kar ta kwana na biyan albashin Febrairu da Maris 2020 na malaman jami'a da suka ki rijista a manhajar IPPIS.”

”Hakazalika ya umurci ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa da Akawunta janar na kasa da su gaggauta biyan kudin domin rage radadin annobar COVID-19 kan lakcarorin da iyalansu.”

”Ana kira ga dukkan shugabannin jami'o'i su sake sanya BVN na lakcarorin kuma su aikewa akawunta janar domin biyansu.”

A baya mun kawo muku rahoton cewa Ministan sadarwa da tattalin arziki da ya dogara da fasahar zamani, Dr Isa Ali Pantami ya sanar da cewa tabbatar da tsarin Integrated Payroll and Personel Information System (IPPIS) ya sa an bankado ma'aikatan bogi har 6,000 a gwamnatin tarayya.

Pantami ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye dalibai karo na 29 a jami'ar fasaha da ke Minna a jihar Neja, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ministan, wanda ya bayyana manufar gwamnatin tarayya na hana ci gaban rashawa a Najeriya, ya kara bayyana cewa gwamnatin tarayya ta adana naira biliyan 24 tun bayan da ta tabbatar da asusun bai daya (TSA) a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel