Yanzu-yanzu: An sallami mutum 1 da ya warke daga cutar Covid-19 a Kaduna
Kwamishinan lafiya ta jihar Kaduna ta sanar da sallamar karin mutum daya wanda ya warke daga cutar Covid-19 a jihar.
Wannan ya kai jimillar wadanda aka sallama a jihar zuwa biyar tun bayan na ranar 14 ga watan Afirilun 2020.
Ta tabbatar da cewa an sake samun wasu mutum 3 da suka kamu da cutar, dukkansu kuwa sun dawo daga tafiye-tafiye ne.
Kamar yadda takardar da ministar ta fitar ta bayyana, "Sun hada da wani matashi mai shekaru 23 wanda ya dawo daga Istanbul bayan ya biyo ta Dubai.
"Dattijo mai shekaru 51 wanda aka gwada a Samaru da ke karamar hukumar Sabon Gari sai kuma wani mai shekaru 42 da ke Unguwan Geza a Kaduna."
Takardar ta kara da cewa, "Wannan sabbin mutanen da suka dauko cutar ta hanyar fita jihar na bayyana hatsarin da ke tattare da yawo zuwa wata jiha a cikin kasar nan.
"Wadannan tafiye-tafiyen na da matukar hatsari saboda ta hanyarsu ne ake kwaso cutar a kaita inda babu.
"A don haka ma'aikatar lafiya ta jihar Kaduna ke kara kira ga jama'ar jihar da su zauna a gida tare da kauracewa tafiye-tafiye don gudun yaduwar annobar."

Asali: UGC
KU KARANTA: Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano
Ma'aikatar lafiyar ta sake tunatar da jama'a amfanin wanke hannu da tsafta don gudun yada kwayar cutar.
A wani labari na daban, Legit.nga ta ruwaito cewa an dakatar da gwajin kwayar cutar Covid-19 a jihar Kano sakamakon rashin kayan aikin.
Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar Covid-19 a Kano ya tabbatar wa da BBC hakan a ranar Laraba.
Ya ce dole ne yasa suka yi hakan don babu sinadaran gwajin kwayar cutar don ci gaba da gwajin a jihar.
Farfesan ya ce a halin yanzu, za a dinga kai samfurin da aka diba na wadanda ake zargin suna dauke da cutar har babban birnin tarayyar Abuja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng