Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar

Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a wani kamfanin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar a jahar Adamawa.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito a yayin harin, yan bindigan sun kashe wasu jami’an Yansanda guda biyu da suka hada da DSP Gbenga da ASP Yohanna.

KU KARANTA: Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwan bamabamai a wani kauyen Neja

Yansandan sun kai ziyara kamfanin Atikun mai suna RicoGado ne domin duba yanayin kamfanin don sanin irin jami’an Yansandan da zasu tura domin samar da tsaro a kamfanin.

Sai dai wani dansanda da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa daga dukkan alamu an shirya kashe Yansandan ne don haka aka shirya musu tarko suka kuma fada.

Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar

Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar
Source: Twitter

A cewarsa: “Sun tafi kamfanin RicoGado ne don duba inda zasu sa jami’an Yansandan da zasu samar da tsaro a kamfanin, isarsu ke da wuya sai dansandan dake gadinsu ya dauki uzuri za shi wani wuri, bai dade da tafiya ba sai wani ya bude musu wuta.”

Kakaakin rundunar Yansandan jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da mutuwar Yansandan biyu, sai dai yace har yanzu basu tabbatar da wanda ya kashe su ba.

“Tabbas an kashe jami’anmu guda biyu masu mukaman DSP da ASP, dangane da wanda ya kashe su kuwa ko kuma inda aka kashe su, ni ma ban sani ba a yanzu, a yanzu dai mun dauko gawarwakinsu, muna jiran samun rahoton yadda aka kashe su.” Inji shi.

A wani labari, Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar.

Daily Trust ta ruwaito yansanda sun kama Sanni Abiodun inkiya Abbey Boy ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel