Kano: 'Yan sanda sun kama matasa 30 da ke buga kwallon kafa

Kano: 'Yan sanda sun kama matasa 30 da ke buga kwallon kafa

A ranar Talata ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da damke matasa 30 da aka samu da laifin take dokar nisantar juna a jihar.

An kama matasan ne da laifin yin kwallon kafa duk da dokar hana cunkoson da gwamnati ta saka don hana yaduwar cutar coronavirus, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da ofishin Dillancin Labaran Najeriya a Kano.

Ya ce an kama wadanda ake zargin a ranar 20 ga watan Afirilun 2020 da karfe 5 na yamma bayan sun kammala buga kwallon kafar a karamar hukumar Dala ta jihar.

A ranar 14 ga watan Afirilun 2020 ne Gwamna Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya.

Hakan na daga cikin hikimar hana yaduwar cutar coronavirus.

Wani bidiyo ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani a ranar Litinin, wanda ke nuna daruruwan matasa na kallon yadda ake taka leda a cikin birnin Kano.

An ga matasa da dama na buga kwallon kafa a wurare da yawa na birnin duk da dokar nisantar juna da gwamnatin jihar ta saka.

Kano: 'Yan sanda sun kama matasa 30 da ke buga kwallon kafa
Kano: 'Yan sanda sun kama matasa 30 da ke buga kwallon kafa
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce

"Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umarnin mika lamarin gaban fannin binciken manyan laifuka na jihar. Bayan kammala bincike za a gurfanar dasu," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya yi kira ga matasan jihar da su mutunta dokar kullen ta jihar tare da nisantar juna don gujewa yaduwar annobar.

Haruna ya ce hukumar ta tsananta sintiri a cikin birnin Kano da sauran sassan ta don tabbatar da an bi dokar hana zirga-zirgar.

"Duk wanda aka kama a titi yana wasan kwallon kafa za a kama shi kuma zai fuskanci fushin hukuma.

"An haramta dukkan taro sannan ba za mu lamunci yawo ba," yace.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa 'yan sandan hadin kai tare da sauran jami'an tsaro ta hanyar kiyaye dokoki.

Ya cigaba da cewa rundunar 'yan sandan za ta tabbatar da an bi dokar kullen don hana yaduwar annobar da ta addabi duniya a jihar.

Hakan ne kadai zai tseratar da rayukan jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng