Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

- Limamai 15 ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke a kan zarginsu da ake da yin sallar Juma'a da jam'i a jihar tare da karya dokar hana zirga-zirga

- Ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tuhumesu sannan an mika wa 'yan sanda lamarin don bincike da hukunci

Limamai 15 ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke a kan zarginsu da ake da yin sallar Juma'a ta jam'i a jihar tare da karya dokar hana zirga-zirga.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada dokar hana zirga-zirga a jihar na tsawon kwanaki bakwai.

A cikin dokar kuwa, akwai haramcin taro kowanne iri har da na addinai da suka hada da sallar Juma'a da taron coci.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Haruna, wanda ya damko wadanda ake zargin a ranar Litinin, ya ce an kama su ne sakamakon zarginsu da ake yi da jan jam'in Juma'a wanda ya saba dokar gwamnatin jihar.

Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a kananan hukumomin birnin Kano, Garko, Gwale, Karaye da Tarauni.

Kano: 'Yan sanda sun dake limamai 15 a fadin jihar

Kano: 'Yan sanda sun dake limamai 15 a fadin jihar
Source: Twitter

KU KARANTA: Kano: Bidiyon dandazon matasa na kwallo duk da doka ya jawo cece-kuce

Ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tuhumesu sannan an mika wa 'yan sanda lamarin don bincike da hukunci.

"An kama wadanda ake zargin ne sakamakon take dokar hana zirga-zirga. Sun ja sallar Juma'a da jam'i a yankunansu.

"An yanke hukuncin kulle jihar da hana zirga-zirga ne bayan an ji ta bakin shugabannin addinai a jihar. Amma wadannan saboda taurin kai suka ja sallar jam'i," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel