Kogi ta Yamma: Kotu ta yi fatali da shakikiyar shaidar Dino Melaye

Kogi ta Yamma: Kotu ta yi fatali da shakikiyar shaidar Dino Melaye

A ranar Talata ne kotun sauraron kararrakin zabe majalisar dattijai ta jihar Kogi, ta yi fatali da shakikiyar shaidar da Dino Melaye ya kawo don kalubalantar zaben yankin Kogi na yamma.

Melaye, wanda shine dan takarar jam'iyyar PDP a zaben ranar 16 ga watan Nuwamban 2019 na kalubalantar sakamakon zaben.

Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ne ya yi nasarar lashe zaben.

A ranar Talata, alkalin da ya jagoranci shari'ar, Isa Sambo ya yi watsi da shaidar Melaye da jam'iyyar PDP.

Alkalin ya ce takardar da shaidar mai suna Mark Samuel ya bada ba ta fito daga hannun shari'a ba.

Kogi ta Yamma : Kotu ta yi fatali da shakikiyar shaidar Dino Melaye
Kogi ta Yamma : Kotu ta yi fatali da shakikiyar shaidar Dino Melaye
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

Kotun ta jaddada sukar da lauyan Adeyemi, Oladapo Otitoju ya yi inda yace takardar da shaidar ya bada ba a gabatar da ita yadda ya dace ba.

Ya kara da cewa, Samuel wanda ya bayyana a matsayin lauya, ya kasa bayyana wata shaida da za ta tabbatar da ikirarinsa.

Otitoju ya ce takardar da shaidar ya gabatar an bada ta ne a ranar 26 ga watan Fabrairun 2020, bayan kwanaki 21 da sashi na 285, sakin layi na biyar na kundun tsarin mulki ya amince.

Ya ce amsar wannan takardar tare da yin amfani da ita na nuna cewa kotun ta kara tsawon kwanakin da kundun tsarin mulki ya bada na shigar da kara bayan zabe.

A hukuncin ranar Talata, Mai shari'a Sambo ya amince da hujjojin Otitoju inda ya yi watsi da Samuel a matsayin shaida.

Wani shaida mai suna Tolu Segun, ya ce ya zama wakilin mai karar a gundumar Okekoko da ke karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar.

Segun ya ce ya kada kuri'arsa ne a akwati na 9 bayan nan ne ya ziyarci akwatuna tara.

Ya ce sakamako da sauran bayanan da ya samo duk sun fito ne daga hannun wani wakili jam'iyyar wanda daga baya suka mika ga shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar.

Za a ci gaba da sauraron karar a ranar Laraba mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel