Zamfara: 'Yan bindiga sun halaka sojoji hudu a karamar hukumar Zurmi

Zamfara: 'Yan bindiga sun halaka sojoji hudu a karamar hukumar Zurmi

- Sojojin Najeriya hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka kai musu

- Lamarin ya faru ne a tsakanin kauyukan Garin-Kada da Birane da ka karamar hukumar Zurmi yayin da dakarun ke hanyar kaiwa 'yan uwansu kayan abinci a cikin daji

- 'Yan bindigar sun halaka sojoji hudu amma sojojin sun halaka 'yan bindigar masu tarin yawa tare da kwace makamansu

Wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe sojoji hudu a karon da suka yi a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya wacce ta san yadda lamarin ya faru ta sanar sa cewa sojojin na kai kayayyakin abinci ne ga abokan aikinsu da ke cikin daji.

Zamfara: 'Yan bindiga sun halaka sojoji 4 a karamar hukumar Zurmi
Zamfara: 'Yan bindiga sun halaka sojoji 4 a karamar hukumar Zurmi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama wadanda aka killace saboda coronavirus suna zina da juna

An gano cewa 'yan bindiga sun biyo sojojin ne a cikin daji wanda yake kusa da kauyukan Garin-Kada da Birane da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar.

Ya ce, "Sun yi amfani da rashin kyan hanyar da ke cikin dajin inda suka labe har zuwa isowar dakarun. Babu jimawa kuwa suka bude wa ababen hawarsu wuta.

"Bayan budewa dakarun wuta, sun kashe hudu daga ciki a nan take. Amma kuma, sojojin sun halaka 'yan bindigar masu tarin yawa tare da kwace makamansu.

"Kwamandan rundunar Operation Hadarin Daji, Birgediya Janar Aminu Bande ya kai ziyara wurin da lamari ya faru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel