Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti bayan warkewa daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti bayan warkewa daga Coronavirus

An samu karin mutane 9 masu cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus da suka samu sauki da lafiya bayan kwashe kwanaki suna jinya a jihar Legas.

Hadimin gwamnan jihar Legas Babajide Sanwoolu, kan sabbin kafafen yada labarai, Jibril Gawat, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita a ranar Talata.

Ya ce an sallamesu ne bayan gwajin karshe da akayi ya nuna cewa sun barranta daga cutar.

Yanzu haka, adadin wadanda aka sallama a Legas ya kai 107.

Yace “Kwamandan yaki da Coronavirus a jihar Legas kuma gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, ya sanar da sallamar karin masu cutar COVID-19 tara.“

“Sun hada da mata 5 da maza. Daga cikinsu akwai wani farin fata dan kasar Poland. Jimillan wadanda aka sallama a yanzu 107.“

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti bayan warkewa daga Coronavirus

Coronavirus
Source: Depositphotos

Duk da irin kai ruwa rana da hukumomin lafiya ke yi domin hana yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, cutar tamkar wutar daji na ci gaba da azuwa a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 25 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Talata 21 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 665 yayin da tuni mutane 188 suka samu waraka.

Ya zuwa yanzu dai mutane 22 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-376; Abuja-89; Kano-59; Osun-20; Oyo-16; Edo-15; Ogun-12; Kwara-9; Katsina-12; Bauchi-7; Kaduna-9; Akwa Ibom-9; Delta-4; Ekiti-4; Ondo-3; Enugu-2; Rivers-2; Niger-2; Benue-1; Anambra-1; Borno-3; Jigawa-2' Abia-2; Gombe-5; Sokoto-1.

Da misalin karfe 11.10 na daren ranar Litinin, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 38 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel