Covid-19: Gwamnatin Katsina ta yi wa mutum 419 da ke gidan gyaran hali rangwame
- Alkalin alkalan jihar Katsina, Mai shari'a Musa Abubakar ya bada belin mutane 419 daga gidan gyaran hali na jihar
- Hakan ya biyo bayan kokarin jihar ne wajen rage cunkoso a gidajen gyaran halin don gujewa yaduwar cutar coronavirus
- Hakazalika, ma'aikatar shari'a ta jihar Katsina ta kirkiro kotu biyu na tafi-da-gidanka don hukunta masu laifuka ko a yayin da dokar hana zirga-zirga ke aiki
Alkalin alkalan jihar Katsina, Mai shari'a Musa Abubakar, ya bada belin a kalla mazauna gidan gyaran hali 419 wadanda suka aikata laifuka daban-daban amma ba a kammala shari'arsu ba.
Gidan talabijin din Channels ya bayyana cewa, wannan ya kasance wani mataki ne na kokarin rage yawan mazauna gidan gyaran halin a jihar.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari
Abubakar ya tabbatar da wannan ci gaban ga gidan talabijin din Channels a ranar Talata, mako daya bayan an rage cunkoson mazauna gidan gyaran halin da ke jihar Katsina.
Ya tabbatar da cewa, an saki mazauna gidan 29 ba tare da wani sharadi ba.
A wani bangare, ma'aikatar shari'a ta jihar Katsina ta kafa wasu kotun tafi da gidanka har biyu a babban birnin jihar don taimakawa kokarin gwamnati na hana yaduwar cutar coronavirus.
Kotun biyu an kafa su ne don gurfanar da masu karya dokar gwamnatin na zaman gida a kananan hukumomin Katsina da Batagarawa na jihar.
Daya daga cikin kotun na nan a yankin shatale-talen Kofar Kaura yayin da dayar ke yankin shatale-talen Kofar Guga duk a babban birnin jihar.
An damke wasu mazauna jihar tare da gurfanar dasu amma daga baya kotun ta sakesu tare da wankesu bayan ta gano ba gaskiya bane zargin da ake musu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng