Mutuwa riga: Jami’in tsaron da marigayi Yar’adua ya baiwa Buhari ya rasu

Mutuwa riga: Jami’in tsaron da marigayi Yar’adua ya baiwa Buhari ya rasu

Wani babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari dake ba shi tsaro, Warrant Officer Lawal Mato ya gamu da ajalinsa a ranar Talata bayan daukan tsawon lokaci yana jinya.

Hadimin shugaban kasa a harkar watsa labaru, Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata,, inda yace Mato ya dade yana jinyar ciwon siga.

KU KARANTA: Babban magana: Shugaban likitocin jahar Sakkwato ya kamu da Coronavirus

“Bayan daukan kimanin shekaru uku yana fama da ciwon siga, guda daga cikin manyan dogaran shugaban kasa Muhammadu Buhari Warrant Officer Lawal Mato ya rasu a ranar Talata.

“Shugaban kasa ya bayyana Mato a matsayin mutumin kirki, kwararre kuma amintaccen Soja da suka dade suna aiki tare tun kafin ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2015, kuma yana aiki kan jiki kan karfi ba tare da wasa ba.

“Shugaban kasa ya yi addu’ar Allah Ya jikan Mato, kuma Ya yi masa rahama, Ya sada shi da alhairan da ya yi a rayuwarsa, sa’anann Ya yi masa rahama da gidan Aljanna.

"Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah Ya baiwa iyalansa da al’ummar Jigawa hakuri da juriyan rashinsa.” Inji shi.

Mutuwa riga: Jami’in tsaron da marigayi Yar’adua ya baiwa Buhari ya rasu
Mutuwa riga: Jami’in tsaron da marigayi Yar’adua ya baiwa Buhari ya rasu
Asali: Facebook

Mato na daga cikin jami’an tsaron da tsohon shugaban kasa marigayi, Umaru Musa Yar’adua ya aikawa Buhari domin su dinga tsaron a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.

Marigayi Yar’adua ya dauki wannan mataki ne bayan Buhari ya kwashe tsawon lokaci a zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ba tare da masu tsaronsa ba.

Wannan babban rashi da shugaba Buhari ya yi ya zo ne a daidai bayan kimanin kwanaki 3 da amininsa, kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ya rasu.

Kyari ya rasu a ranar Juma’a a jahar Legas sakamakon kamuwa da ya yi da cutar Coronavirus, annobar nan mai toshe numfashi wanda a yanzu haka ta zama ruwan dare a duniya.

Kyari ya rasu yana da shekaru 67 a duniya, ya bar mace 1, Hajiya Kulu da yara hudu, sai kuma tarin yan uwa a jahar Borno da abokan arziki a duk fadin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel