Mutanen da cutar coronavirus ta kashe sun haura 170,000 a duniya - Alkalumma
Alkalumma sun tabbatar da cewa annobar coronavirus ta hallaka fiye da mutane 170,000 a fadin duniya. Kusan kaso 2 cikin 3 na mace-macen sun auku ne a nahiyyar Turai.
Mutane 170,226 ne suka riga mu gidan gaskiya a fadin duniya a sanadiyar cutar corona wadda ta zamto ruwan daren da ya dugunzuma al'ummomi.
Kididdigar alkalumma ta nuna cewa, mutane 106,737 suka halaka saboda cutar corona a nahiyyar Turai kadai.
Yayin da mutane 42,364 suka mutu a kasar Amurka inda mace-macen ya fi ta'azzara, kasar Italiya ta samu adadin mutane 24,114 da mai yankan kaunar ta rufawa bargo.
Haka kuma an samu mace-macen mutane 21,282 a kasar Spain yayin da mutane 20,265 suka kwanta da dama a kasar Faransa da kuma mutane 16,509 a kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labarai na Duniya AFP ya ruwaito cewa, a yanzu haka mutane 2,483,086 ne suka harbu da cutar corona a fadin duniya.

Asali: UGC
Kamfanin ya tattaro wannan kididdiga ta alkalumma daga taskar bayanai ta Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Idan muka waiwayo nan gida Najeriya, adadin wadanda cutar ta harba sun kai 665 kamar yadda Hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar ta bayyana a daren ranar Litinin.
KARANTA KUMA: Kasashe 12 masu amfani da fasahar 5G a yanzu
Yanzu haka dai cutar ta bulla a jihohi 25 na kasar inda na baya-bayan nan suka kasance Borno, Abia, Sakkwato da kuma jihar Gombe.
A yayin da dokar hana fita ta jefa da yawa daga cikin wasu al'ummomi cikin ha'ula'i da rashin sakewa, WHO ta gargadi kasashen da ke yunkurin janye dokar kullen da suyi kaffa-kaffa.
Hukumar ta gargadi kasashen a kan kada su yi garajen janye dokar hana zirga-zirga, lamarin da ta ke aiwatar da hakan na iya mayar da hannun agogo baya.
WHO ta yi gargadin cewa kasashe su jingine kudirin su na janye dokar tilasta zaman gida har sai an samu allurar riga-kafin cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng