Hanyoyin kaucewa rushewar Najeriya da dokar hana fita za ta haifar

Hanyoyin kaucewa rushewar Najeriya da dokar hana fita za ta haifar

A halin yanzu gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar annobar coronavirus wadda ta yiwa duniya lullubi.

A yunkurin haka gwamnatocin kasashe da dama na Turai da kuma na nan gida a nahiyyar Afirka, sun dauki matakin shimfidawa al'ummomin su dokar tilasta zaman gida.

Kuma da yawa daga cikin gwamnatocin sun yaba wa al'ummomin su sanadiyar yiwa wannan doka da'a da kuma samun hadin kansu yayin da ake fafutikar dakile yaduwar cutar.

Sai dai wani rahoto da muka samu daga sashen Hausa na BBC dangane da ababen da ke faruwa a jamhuriyyar Nijar da kasar Amurka ya sha ban-ban da sauran kasashe.

Mun ji cewa zanga-zanga ta barke a jamhuriyyar Nijar da kuma kasar Amurka ta nuna rashin goyon baya a kan dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin kasar ta shimfida.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasa a birnin Yamai da ke jamhuriyyar Nijar sun bazama wajen gudanar da zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da dokar gwamnati ta hana zirga-zirga.

Gwamnatin Nijar ta shimfida dokar hana fita wadda ta ke fara aiki daga karfe 7.00 na Yammaci zuwa 6.00 na safiyar kowace rana.

Har ta a daren ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu, matasan Yamai sun cinna wuta a unguwanni bakwai, lamarin da ya janyo jami'an tsaro suka yi musu tarnaki da barkonon tsohuwa.

Rashin nuna goyon baya ya sanya matasan suka bijire wa dokar hana fita na gwamnatin, inda suke ci gaba da karade tituna tare da kona tayoyi da lalata ababen more rayuwa.

Lamarin bai takaita a nan kadai ba domin kuwa mashaida sun tabbatar da cewa matasan bayan zanga-zanga sun kuma koma far wa dukiyoyin al'umma.

Sai dai ana zargin cewa da alama har yanzu mutane da dama a nahiyar Afirka ba su yarda akwai cutar corona ba duk da irin durkusar da al'ummomi da ta ke ci gaba da yi a fadin duniya.

Matasa yayin zanga-zanga a birnin Yamai saboda dokar takaita zirga-zirga

Matasa yayin zanga-zanga a birnin Yamai saboda dokar takaita zirga-zirga
Source: Getty Images

Haka kuma kasar Amurka, an gudanar da zanga-zanga a jihohin Colorado, Arizona, Motana, da kuma babban birnin Washington.

Wannan sabuwar zanga-zanga da aka gudanar a ranar Lahadi ta biyo bayan wasu makamantanta da aka gudanar a jihohi shida na kasar.

Al'ummar kasar sun nemi gwamnati ta saukaka dokar hana fita duk da hadarin kamuwa da cutar muddin aka bude makarantu, hanyoyi da ofisoshi.

KARANTA KUMA: Jerin kasashen da suka fi kamu wa da cutar coronavirus a nahiyyar Afirka - WHO

Sai dai sabanin yadda ake tunani, shugaban kasar Donald Trump, ya nuna amincewarsa da zangar-zangar da mutanen kasar ke gudanarwa.

Masu hangen nesa na ganin cewa muddin aka ci gaba da tafiya a haka, al'ummomi da dama za su yi bore da ka iya haifar da rushewar kasashe saboda dokar da babu shakka ta hana su sakewa.

Dokar tilasta zaman gida musamman a kasar Najeriya wadda duniya ta ke yiwa lakabi da madubi na talauci, ta jefa al'ummar kasar cikin yanayi na ha'ula'i.

A yayin da kawo yanzu ba a gano maganin cutar corona ba, abu mafi a'ala shi ne saukaka dokar takaita zirga-zirga tare da shimfida matakan hana cudanyar mutane ta hanyar bayar da tazara.

Ga wasu matakai shida (6) da ya kamata gwamnati ta dauka domin kaucewa rushewar Najeriya da dokar hana fita za ta iya haifarwa:

1. Cire dokar hana fita tare da ci gaba da dokar hana cudanya da bayar da tazara a tsakanin mutane.

2. Bayar da tazara ta tsawon mita shida a tsakanin mutane a wuraren da ke tara jama'a kamar kasuwa, makarantu da wuraren aiki.

3. Tabbatar da kowa ya sanya takunkumin hanci da safar hannu yayin fita

4. Takaita fita da kananan yara matukar fita da su ba ta zama tilas ba.

5. Halartar wurin ibadu da makarantu kuma a tabbatar mutanen da za su halarta ba su wuce hamsin ba walau a masallaci da dakunan karatu.

6. Gwamnatin Najeriya ta nemi agajin hukumomin kula da tattalin arziki na Duniya kamar Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni na Duniya, IMF, domin samun saukin radadin da kasar ke fuskanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel