Hankula sun tashi a Kano bayan mutum 150 sun rasu a cikin kwana 3
A kalla mutum 150 ne suka rasa rayukansu tsakanin ranar Juma'a da Asabar na makon da ya gabata a garin Kano.
Wannan tururuwar birne jama'ar ne ya saka tsananin tsoro da fargaba a zukatan mazauna jihar don basu san takamaiman abinda ya jawo mutuwar ba.
Masu hakar kaburbura a makabartun birnin Kano sun ce yawan gawawwakin da aka kai makabartun ya fi yadda suka saba birnewa kafin barkewar annobar Coronavirus.
Hukumomi a jihar Kano, shugabanni, iyalan mamatan da kuma ma'aikatan lafiya na jihar sun bada labari mabanbanta game da mace-macen.
Wakilin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa wannan ci gaban ya matukar girgiza zukatan mazauna birnin Kano don sun fara zargin cewa annobar ce ke dibar rayuka a cikin jihar.
A cikin kananan hukumomin da aka samu wannan mace-macen akwai Nasarawa, Gwale, Dala, Ungogo, Fagge, Tarauni, Kumbotso da birnin Kano.
Masu hakar kabari sun ce lamarin da matukar bada tsoro don haka ne suke kira ga gwamnatin jihar da ta bincika dalilin mace-macen.
Bashir Mohammed, daya daga cikin masu hakar kabari a makabartar Dandolo da ke Goron Dutse, karamar hukumar Dala ta jihar Kano, yace, "Wannan abun fargaba ne kuma ya matukar girgiza mu. Yadda jama'a ke mutuwa ya zarce misali."

Asali: Twitter
KU KARANTA: Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya
Mohammed wanda aka fi sani da Mai Sana'a, ya ce tsakanin ranar Asabar da Lahadi, a kalla mutane 30 aka birne a makabartar. Hakan kuwa ya ci karo da yadda aka saba.
Mohammed ya ce mamatan dai da yawan su tsoffi ne daga dukkan jinsi biyun.
Hakazalika, a makabartar mayanka da ke kusa da Kofar Mazugal, an tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa an birne mutum 61 a cikin ranakun karshen makon.
Masu tsaron makabartar sun ce da yawan mamatan daga Zage, Darma, Sharifai, Gabari da kuma Zangon Barebari suke na birnin Kano.
Da yawa daga cikin 'yan uwan mamatan sun ce zazzabin cizon sauro mai zafi ne da kuma cutar taifot ce ta yi ajalin 'yan uwan nasu.
Wasu mazaunan yankunan kuwa sun danganta mace-macen da rufe asibitoci masu zaman kansu da gwamnatin jihar tayi sakamakon bullar cutar coronavirus.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng