Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla Sakkwato birnin Shehu

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla Sakkwato birnin Shehu

An samu bullar cutar Coronavirus a Sakkwaton Shehu, Gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a jawabin da yayiwa manema labarai da daren Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2020.

A cewarsa, mutumin d aya kamu na kwance a asibitin koyarwan jami'ar Usamnu DanFodio, dake jihar.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Sokoto, cikin bakin ciki nike mai sanar muku da labaran cewa an samu bullar annobar Coronavirus a nan jihar Sokoto."

"Tunda an tabbatar da kamuwa mutumin, za'a kai shi cibiyar killacewa dake Amanawa."

"Ina kira ga al'ummar jiharmu su cigaba da biyayya ga shawarin da jami'a kiwon lafiya suka bada domin takaita yaduwar cutar."

"A da labarinta muke ji, amma ga ta nan ta iso wajenmu. Saboda haka ya zama wajibi su zange dantse a matsayin gwamnati wajen hanata yaduwa."

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla Sakkwato birnin Shehu

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla Sakkwato birnin Shehu
Source: Twitter

A jiya, an samu bullar cutar a jihar Borno da Jigawa kuma tuni na jihar Bornon ya mutu. Mamacin ma'aikacin majalisar dinkin duniya ne.

Majalisar dinkin duniya (UN) ta ce ma'aikacinta da cutar covid-19 ta hallaka a jihar Borno bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

Edward Kallon, jagoran harkokin aiyukan taimako na UN a Najeriya, ya ce su na kokarin bin sahun duk mutanen da marigayin ya yi mu'amala da su kafin mutuwarsa.

A ranar Lahadi ne rahotanni su ka bayyana cewa wani ma'aikacin UN ya mutu a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan an kwantar da shi sakamakon nuna alamomin rashin lafiya irin na cutar covid-19.

"Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa ne wajen taimakon mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijia.

"Bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

"Hukumomin aiyukan jin kai a karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO) su na aiki tare da NCDC, gwamnatin jihar Borno, ma'aikatar lafiya ta kasa da sauran ma su ruwa da tsaki wajen bin sahun mutanen da ya yi mu'amala da su," a cewar Kallon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel