Batun sauya ma jami’ar jahar Imo suna zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna

Batun sauya ma jami’ar jahar Imo suna zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna

Gwamnatin jahar Imo ta musanta labaran dake yawo wai za ta sauya sunan jami’ar jahar Imo zuwa jami’ar Abba Kyari, ba kamar yadda rahotanni suke ta yayatawa ba.

Gwamnan jahar Imo, Sanata Hope Uzodinma ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace wannan ba wani abu bane illa labarun kanzon kurege.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Najeriya za ta fara kwaso yan kasar waje daga mako mai zuwa

Sahara Reporters ta ruwaito gwamnan ta bakin kakaakinsa, Oguwike Nwachuku yace tun bayan mutuwar Kyari aka samu wani dake ta fitar da labarun karya da sunan gwamnatin Imo.

Batun sauya ma jami’ar jahar Imo zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna
Batun sauya ma jami’ar jahar Imo zuwa jami’ar Abba Kyari karya ne – Gwamna
Asali: Facebook

“Mutumin yana amfani da suna Mista Nwachuku, kuma yayi amfani da alamar gwamnatin jahar Imo yana ta watsa labarun karya domin yaudarar mutanen jahar Imo don su yarda da karairayinsa.

“A irin wannan labarun karyar ne suka danganta gwamnan jahar Imo da wani rahoton cewa wai zai sauya sunan jami’ar jahar Imo zuwa jami’ar Abba Kyari don ya girmama tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya.

“A karyarsu, gwamnan zai yi hakan ne domin karrama Kyari saboda shi ne ya yi sanadiyyar zamansa gwamnan jahar Imo. Da wannan muke kira ga jama’a da su lura da abubuwan da suke karantawa don kauce ma fada ma tarkon labarun karya.

“Kuma su dage wajen gano masu yayata wadannan labaru tare da tabbatar da sun bada gudunmuwa don ganin an kawo karshen labarun kanzon kurege a duniya gaba daya.” Inji shi.

A wani labari kuma, Jama’tul Nasril Islam ta yi kira ga Musulman Najeriya su saurari sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar kafin su dauki azumin watan Ramadan.

Sakataren jama’atu, Sheikh Khalid Aliyu ne ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda yace Sarkin Musulmi ne kadai ke da hakkin sanar da ganin watan Ramadan.

Don haka Khalid ya nemi Musulmai su nemi wata, sa’annan su sanar da shuwagabannin addinin Musulunci mafi kusa domin a sanar da Sarkin kafin a sanar ma al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel