Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 100 a kauyen Buni Gari da ke karkashin karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

A wani jawabi da kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, ya fitar ranar Lahadi a Damaturu, ya ce an kashe mayakan kungiyar Boko Haram yayin da su ke shirin kaddamar da wani babban hari a kauyen.

Kauyen Buni Gari bashi da nisa daga wata makarantar rundunar soji da ke Bunu Yadi, wacce kuma kuma aka jibge rundunar soji ta musamman domin yaki da 'yan ta'adda a jihar Yobe.

Kanal Musa ya ce dakarun soji a karkashin jagorancin, Janar Lawrence Araba, sun samu nasarar cimma mayakan kafin su kaddamar da harin da su ka shirya kaiwa.

Ya bayyana cewa dakarun soji sun samu sahihan bayanan sirri a kan shirin mayakan na kai hari kauyen ranar Asabar.

Da ya ke nuna wa babban hafsan rundunar sojin kasa, Janar Tukur Buratai, irin makaman da aka samu a wurin mayakan da aka kashe, Janar Araba, ya ce an kashe mayakan Boko Haram 105.

A jawabinsa, Buratai ya yabawa sojoji kafin daga bisani ya wuce zuwa sansanin sojoji na Damaturu domin duba sojojin da su ka samu raunuka yayin gumurzun da su ka yi mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Makaman 'yan Boko Haram
Source: Twitter

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe
Source: Twitter

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 a Yobe
Source: Twitter

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Gawar dan Boko Haram
Source: Twitter

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram fiye da 100 yayin wani gumurzu a Yobe (Hotuna)

Gawar dan Boko Haram
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel