An binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko mai Corona a Borno

An binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko mai Corona a Borno

Gwamnatin jahar Borno ta samu nasarar binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko da ya kamu da annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wani jami’in kiwon lafiya ne ya fara kamuwa da cutar a jahar Borno, inda ta yi sanadiyyar mutuwarsa a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

KU KARANTA: Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona

Wannan jami’in kiwon lafiya yana aiki ne da kungiyar likitoci mai zaman kanta, watau Doctors without borders a kauyen Pulka cikin karamar hukumar Gwoza, inda ya rasu a ranar Asabar.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jahar Borno, Umar Kadafur ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake ganawa da manema labaru a Maiduguri.

An binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko mai Corona a Borno

Jami'an NCDC
Source: Twitter

“Muna bin sawun duk wadanda mutumin ya yi mu’amala dasu don daukan matakan da suka kamata domin gudun yaduwar cutar a cikin al’umma, zuwa yanzu mun gano mutane 99, kuma an fara musu gwaje gwaje, 35 a Pulka, 64 a Maiduguri.

“Haka zalika an umarci kungiyar da yake ma aiki a Pulka ta mika sunayen duk ma’aikatanta, kuma ta killace su duka, zuwa yanzu an tura tawagar likitoci domin lura da mutanen tare da daukan abubuwan da ake bukata na yin gwaji daga wurinsu” Inji shi.

Umar Kadafur ya yi kira ga jama’a su dauki batun annobar nan da muhimmanci, kuma su bi dokokin da aka shimfida don tsaftace jikinsu, muhallansu tare da kauce ma shiga cikin jama’a.

Zuwa daren litinin, gwamnan jahar, Farfesa Babagana Umara Zulum zai gabatar da jawabi ga jama’an jahar, a hannu guda kuma an kama mutane 85 da suka karya dokar shige da fice a jahar.

Rahotanni sun bayyana tuni gwamnatin jahar ta killace su tsawon kwanaki 14 domin tabbatar da matsayinsu dangane da kasantuwar cutar a tattare da su ko kuwa a’a.

A wani labari kuma, Kamfanin wutar lantarki ta Kaduna ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna a jahohin da take raba ma wuta har sai an shawo kan annobar COVID-19.

Shugaban sashin watsa labaru na hukumar Abdulazeez Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labaru a ranar Litinin yayin mika taimakon kayan tallafin ga gwamnatin Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel