Da duminsa: An sake sallamar mutum na 7 daga asibiti bayan samun waraka daga Coronavirus

Da duminsa: An sake sallamar mutum na 7 daga asibiti bayan samun waraka daga Coronavirus

Gwamnatin jihar Edo a ranar Litinin a babbar birnin jihar, Benin, ta sanar da sallamar mutum na bakwai mai fama da cutar Coronavirus bayan samun waraka.

Gwamnan jihar, Godwin Obaseki, wanda yayi sanarwar ya ce mutumin ne wanda ya kawo cutar Coronavirus jihar kuma Alhamdulillahi ya samu sauki.

Obaseki ya ce kashi 50% na wadanda suka kamu da cutar a jiharsa sun samu sauki kuma an sallamesu.

Yace “Wani mai cutar COVID-19, wanda shine mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Edo, ya samu waraka bayan gwajin da akayi masa.“

“An sallamesa kuma ya koma cikin iyalansa.“

“Yanzu adadin wadanda muka yi jinya kuma muka sallama daga cibiyar killacewarmu ya kai bakwai. Rabin mutanen da ke dauke da cutar a asibitocinmu sun warke.“

KU KARANTA Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus

Da duminsa: An sake sallamar mutum na 7 daga asibiti bayan samun waraka daga Coronavirus

Coronavirus
Source: Facebook

A bangare guda, Majalisar dinkin duniya (UN) ta ce ma'aikacinta da cutar covid-19 ta hallaka a jihar Borno bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

Edward Kallon, jagoran harkokin aiyukan taimako na UN a Najeriya, ya ce su na kokarin bin sahun duk mutanen da marigayin ya yi mu'amala da su kafin mutuwarsa.

A ranar Lahadi ne rahotanni su ka bayyana cewa wani ma'aikacin UN ya mutu a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan an kwantar da shi sakamakon nuna alamomin rashin lafiya irin na cutar covid-19.

"Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa ne wajen taimakon mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira."

"Bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno."

Hukumar NCDC ta tabbatar da bullar cutar Coronavirus ne a jihar Borno a daren Lahadi, 19 ga watan Afrilu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel