Covid-19: 'Yan KAROTA sun kama mutane 350, motoci 35 a Kano

Covid-19: 'Yan KAROTA sun kama mutane 350, motoci 35 a Kano

Hukumar kula da cunkuson ababen hawa a Kano (KAROTA) ta ce ta kama a kalla mutane 350 da suka saba dokar nesanta da aka sakawa ababen hawa na haya a jihar.

Tun bayan bullar annobar covid-19 a Kano, gwamnatin jihar ta saka dokar rage yawan fasinjoji zuwa biyu a doguwar kujera daya ta motocin haya.

Kakakin hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar, ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), a ranar Litinin, cewa sun kama motoci 35.

NAN ta rawaito cewa gwamnatin Kano ta umarci motocin haya su rage yawan fasinjojin da su ka saba dauka tare da bawa babura ma su kafa uku (adaidaita) umarnin daukan mutane biyu kacal.

A cewar NAN, gwamnatin Kano ta dauki wannan mataki ne don dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar.

Covid-19: 'Yan KAROTA sun kama mutane 350, motoci 35 a Kano
Covid-19: 'Yan KAROTA sun kama mutane 350, motoci 35 a Kano
Asali: Twitter

A cewar Abubakar, su na umartar mutanen da su ka kama suka shigo Kano da su koma inda su ka fito.

Ya kara bayyana cewa za a gurfanar da direbobin motocin da aka kama a gaban kotu da zarar an janye dokar zaman gida.

Kakakin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar KAROTA ba ta kama dan adaidaita ko daya ba a kan saba doka.

DUBA WANNAN: Murnar mutuwar Kyari: Kwamishinan da Ganduje ya tube ya yi magana a karo na farko

A wani labarin da ya shafi Kano da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin jihar ta yi watsi da rade-radin da ke yawo kan cewa mutane na mutuwa birjik a jahar a 'yan kwanakin nan.

A wani rabutu da ma’aikatar lafiya ta jahar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin jita-jitan.

Ta bayyana hakan a matsayin aikin masu yada zantuka marasa tushe.

Ma’aikatar lafiyar ta jaddada cewa ta na daukar matakai da suka kamata domin ganin ta dakile annobar COVID-19 a jahar. Ta kuma ce ta na da karfin gwiwa a kan yaki da take yi da annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel