Ya kamata gwamnati tayi bincike a kan mutuwar Abba Kyari - Falana

Ya kamata gwamnati tayi bincike a kan mutuwar Abba Kyari - Falana

- Babban Lauya a Najeriya, Femi Falana, ya nemi gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan mutuwar Abba Kyari

- Falana ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike kan mutuwar Abba Kyari duba da yadda yayi jinya a wani asibitin kudi da hakan na cin karo da ka'idar Hukumar Lafiya

Wani babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Babban lauyan ya nemi gwamnatin da ta gaggauta aiwatar da bincike a kan ababen da suka dabaibaye jinya da kuma mutuwar marigayi Kyari.

Falana ya ce bukatar aiwatar da binciken ta zo ne duba da yadda aka yi jinyar marigayi Kyari a wani asibitin kudi sabanin yadda Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya shar'anta.

A baya dai Mista Ehanire ya ce babu wani asibitin kudi a fadin kasar nan da aka yiwa lamunin duba lafiyar duk wani wanda cutar coronavirus ta harba kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Marigayi Mallam Abba Kyari da Femi Falana
Marigayi Mallam Abba Kyari da Femi Falana
Asali: UGC

Lauya Femi ya ce wannan ce madogararsa ta neman gwamnati ta gudanar da binciken gaggawa kan mutuwar mai lura da al'amuran ma'aikatan fadar shugaban kasa da ajali ya katsewa hanzari.

Lauyan ya ce duba lafiyar marigayi Mallam Kyari da aka yi a asibitin kudi ya sabawa ka'aidoji da kuma sharuddan da aka gindaya kan annobar cutar covid-19.

KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnati ta fara kwashe Almajirai daga birnin Kano

Ya ce manya a Najeriya da cutar coronavirus ta harba na ci gaba da matsin lamba ta lallai sai an duba lafiyarsu tare da yin jinya a asibitocin kudi, lamarin da ya ce hakan ya sabawa ka'ida.

Shahararren lauyan ya kuma bayyana takaicinsa dangane da yadda mutanen da suka halarci jana'izar marigayi Kyari suka sabawa ka'idojin killace kai na hana yaduwar cutar coronavirus.

Ana iya tuna cewa Mai Duka ya karbi rayuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Juma'a 17 ga watan Afrilun 2020, bayan ya sha fama da cutar corona.

A yayin da ya zuwa yanzu a ke ci gaba da alhinin mutuwarsa, shugabannin duniya da dama sun aikewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari sakonninsu na ta'azziya gami da rarrashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel