Covid-19: Gwamnati ta fara kwashe Almajirai daga birnin Kano

Covid-19: Gwamnati ta fara kwashe Almajirai daga birnin Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni dai gwamnati ta fara kwashe Almajirai daga birnin Kano zuwa mahaifarsu.

Gwamnatin Kano ta dauki wannan mataki a ci gaba da yunkurin da take yi na dakile yaduwar cutar coronavirus, wadda ta bulla a jihar makonni kadan da suka gabata.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito, furucin wannan mataki ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje ya bayar da shaidar hakan a ranar Lahadi yayin ganawa da kwamitin da ke tattara tallafi da kuma gudunmuwar da aka samu ta rage radadin annobar coronavirus.

Ya ce gwamnatinsa ta kafa kwamitin kula da wannan kudiri bisa jagorancin kwamishinan kananan hukukomi na jihar, Murtala Sule Garo.

A cewar sa, "Mun rufe dukkanin makarantu saboda dakile yaduwar wannan annoba sai dai mun fahimci cewa makaratun Almajirai na mayar mana da hannun agogo baya."

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

"Muna da masaniyar adadin Almajirai muna kuma da rajistar dukkanin makarantun Almajirai dake fadin jihar. Ya zuwa yanzu fiye da Almajirai 2000 sun koma jihohinsu."

Gwamna Ganduje ya ce za a mayar da Almajiran zuwa mahaifarsu musamman wadanda suka fito daga jihohin dake makwabtaka da Kano.

Ya ce akwai tarin Almajirai a Kano wadanda suka fito daga jihohin Katsina, Bauchi, Jigawa, Kaduna da kuma kasar Nijar.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar Afirka za ta zama cibiyar coronavirus - WHO

Tare da hadin gwiwar sarakunan gargajiya, Ganduje ya ce an zakulo magidanta masu tsananin bukatar taimako fiye da 50,000 wanda gwamnati za ta tallafa masu da kayan agaji.

Ya ce za a rarraba wa kowane daya daga cikin mabukatan buhun shinkafa, garin masara, taliya, man gyada da kuma Naira dubu biyu.

Tun bayan bullar cutar coronavirus karo na farko a jihar a ranar 11 ga watan Afrilu, ya zuwa yanzu akwai mutane 36 da cutar ta harba kamar yadda alkalumman Hukumar Lafiya suka tabbatar.

Ci gaba da yaduwar cutar ta sanya gwamnatin Kano tun a daren ranar Alhamis ta makon da ya gabata, ta dauki mataki na shimfida dokar hana fita har na tsawon kwanaki bakwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel