An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari

An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari

Bayan gama janaizar Mallam Abba Kyari a ranar Asabar 18 ga watan Afrilu, tuni dai an fara zawarcin wanda zai maye kujerar mai karfi ta shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa cikin sirri.

An fara ambaton sunayen mutanen da ake ganin za su iya maye gurbin Kyari da ya rasu bayan ya kamu da cutar coronavirus kuma ya yi jinya na wasu makonni kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A fadar shugban kasar an fara ambaton sunayen mutane da suka hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, Ministan Ilimi, Adamu Adamu da shugaban Kwastam, Hamid Ali a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Kyari.

An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari

An fara zawarcin kujerar marigayi Abba Kyari
Source: Twitter

1. Babagana Kingibe – Tsohon dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a karkashin jamiyyar Social Democratic Party (SDP) a 1993. Yana da shekaru 74 da haihuwa. Shugaba Buhari ya taba karrama shi da lambar yabo ta (GCON).

2. Hamid Ali – Tsohon shugaban mulkin soji na jihar Kaduna ya rike mukamin shugaban ma'aikatan fadar Buhari har zuwa lokacin da aka nada Kyari a shekarar 2O15. An haife shi ne a shekarar 1955. Nada shi shugaban kwastam ya gina shamaki tsakaninsa da shugaban kasar.

3. Adamu Adamu – Tsohon marubuci ne a jaridar Daily Trust kuma yana daga cikin aminan shugaban kasa. Ya rike mukamin sakataren kwamitin karbar mulki a shekarar 2O15 lokacin da Buhari ya ci zaben shugaban kasa.

Abubuwan da ya dace Buhari ya yi la'akari da su

Dattijan arewa, yan siyasa kuma masu nazarin al'amuran yau da kullum sun yi nazarin wasu abubuwa da ya dace Shugaba Buhari ya lura da su wurin zaben wanda zai maye gurbin Kyari.

Wani Dattijo ba ya nemi a boye sunansa ya yi kira ga shugaban kasar ya zabi matashi mai basira da hazaka domin maye gurbin Kyari.

A hirar da ya yi da Daily Trust a ranar Lahadi, ya ce, "Shugaban kasa yana bukatar matashi kuma dan siyasa wanda ya fahimci yadda al'amura ke tafiya a kasar.

"Duk wanda zai zama shugaban maaika sai ya san kasar nan ciki da waje. Ya kamata Buhari ya duba inda muka fito da inda za mu nufa da abinda zai iya yi domin yi wa gwamnatinsa garambawul."

Muna bukatar mutum mai tausayi kuma wanda zai iya fada shugaban kasa cikin hikima cewa, "A'a ba zamu iya aikata wannan abin ba," Ya kuma iya fada masa cewa, "Eh, zamu iya aikata wannan abin."

Kazalika, Sanata Abu Ibrahim wanda na kusa da shugaban kasa ne ya bayyana Kyari a matsayin mutum mai matukar basira da jajircewa wurin aikinsa.

Ya ce, "Buhari ba mutum bane mai garaje. Na tabbata zai zabi mutumin da ke da akida irin tasa na cigaban kasar nan. Ina adduar fatan shugaban kasa ya zabi wanda ya dace."

Muhimmin aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa kamar yadda shafin intanet na gidan gwamnati ta wallafa shine lura da sukkan abubuwan da ke wakana a ofishin shugaban kasa.

Kazalika, aikinsa ya hada da tantance ayyukan yau da kullum da shugaban kasa zai yi da kuma sakonnin da za su isa ga shugaban kasar da wadanda za su fita daga ofishin shugaban kasar da kuma duk wani aiki da shugaban kasar ya umurci shi ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel