An samu gawar mayakan Boko Haram 44 a gidan yari

An samu gawar mayakan Boko Haram 44 a gidan yari

A ranar Asabar ne babban mai gabatar da kara a gaban kotu na kasar Chadi ya sanar da cewa an samu gawar wasu mayakan kungiyar Boko Haram su 44 da aka kama kwanan nan yayin wani atisaye.

Da ya ke magana a gidan talabijin na gwamnati, Youssouf Tom ya ce, an samu gawar mutanen ne ranar Alhamis da safe, a cikin dakin da su ke kulle.

Ya kara da cewa su mutanen 44 na daga cikin mutum 58 da dakarun soji na hadin gwuiwa su ka kama yayin wani atisaye a yankin tekun Chadi.

"An kama mambobin kungiyar Boko Haram 58 yayin wani atisaye na kwanakin baya bayan nan a yankin tekunChadi, an tura dukkansu gidan yari da ke Ndjamena kafin a kammala bincike.

"Amma sai labari ya same mu da safiyar ranar Alhamis a ranar cewa an samu gawar 44 daga cikinsu a cikin dakin da aka kulle su," a cewar Tom.

An samu gawar mayakan Boko Haram 44 a gidan yari

Wasu mayakan Boko Haram da aka yankewa hukuncin kisa a kasar Chadi
Source: Twitter

Kazalika, ya bayyana cewa ya halarci har dakin da aka kullesu a gidan yarin bayan ma su kula da su sun sanar da shi mutuwarsu.

DUBA WANNAN: Manyan annoba 6 da aka taba yi a duniya da adadin mutanen da kowacce ta hallaka

Ya bayyana cewa su na gudanar da bincike domin gano yadda fursunonin su ka mutu.

"Mun binne 40 daga cikinsu, yayin da mu ka tura sauran 4 zuwa asibiti domin gudanar da binciken gano musabbabin mutuwarsu," a cewarsa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na APF ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel