Aisha buhari ta yi martani a kan mutuwar Mallam Abba Kyari

Aisha buhari ta yi martani a kan mutuwar Mallam Abba Kyari

- Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi ta’aziyya ga iyalan Abba Kyari, marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa

- A wata wallafa da ta yi a shafinta na twitter, uwargidan shugaban kasan ta mika ta'aziyyarta ga Kulu Abba Kyari da daukacin iyalansa

- Ta kara da yin addu'ar samun sauki ga wadanda ke fama da cutar tare da fatan Allah ya kawo karshen annobar

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi ta’aziyya ga iyalan Abba Kyari, marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

A ranar Juma’a ne fadar shugaban kasa ta sanar da mutuwar Kyari sakamakon cutar coronavirus.

A wata wallafa da ta yi a shafinta na twitter, uwargidan shugaban kasan ta ce: “Daga Allah muke kuma gareshi za mu koma. Ina ta’aziyya ga Kulu Abba Kyari da daukacin iyalan marigayin a kan rashinsa da aka yi.”

“Ina fatan Allah ya yafe masa kura-kuransa, ya saka masa da gidan Aljannar Firdausi sannan ya bada hakurin jure rashinsa. Ameen

“A yayin da nake fatan samun sauki ga dukkan masu fama da cutar, ina rokon Allah ya kawo mana karshen annobar,” ta ce.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami kwamishinansa da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari

Abba Kyari haifaffen dan kabilar Kanuri ne daga jihar Borno da ke Arewa maso gabas din Najeriya. Ya samu karatun firamare da na sakandare a jihar Borno.

Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Warwick ta Ingila a fannin halayyar dan Adam a 1980.

Hakazalika, ya sake kammala wani digirin a fannin shari'a daga jami'ar Cambridge.

Ya zama lauya a shekarar 1983, bayan ya halarci makarantar horar da lauyoyi ta Najeriya.

A shekarar 1984, Kyari ya kammala digirinsa na biyu a fannin shari'a daga jami'ar Cambridge.

Daga baya, ya halarci kwalejin gudanarwa ta Lausanne da ke Switzerland a 1992. Ya sake halartar horarwa a kan gudanarwa da ci gaban al'umma a makarantar koyar da kasuwanci ta Harvard a 1994.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel