COVID-19: Mutum 3 sun sake rasuwa a jihar Legas

COVID-19: Mutum 3 sun sake rasuwa a jihar Legas

Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wasu mutum 3 masu cutar coronavirus. Kwamishinan lafiya na jihar, Akin Abayomi ne ya sanar da labarin a ranar Asabar.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, ya ce wadanda suka rasun sun hada da maza biyu da mace daya, jaridar The Cable ta wallafa.

Ya kara da cewa, biyu daga cikinsu na da wani ciwo na daban kafin samuwar coronavirus din.

"An sake tabbatar da cewa wasu mutum 32 na dauke da cutar coronavirus a jihar Legas a ranar 17 ga watan Afirilun 2020. A halin yanzu mutum 286 ne suka kamu," yace.

"Abin takaici, mutum uku sun sake rasuwa sakamakon cutar a jihar Legas.

"Mamatan sun hada da maza biyu da mace daya kuma dukkansu sun wuce shekaru 50 a duniya. An gano biyu daga ciki na dauke da wasu cutuka kafin samuwar coronavirus.

"Mazan biyu sun kamu ne bayan mu'amala da suka yi da me cutar.

"Macen kuwa ta samu cutar ne daga tafiyar da tayi zuwa kasar waje," Kwamishinan yace.

COVID-19: Mutum 3 sun sake rasuwa a jihar Legas
COVID-19: Mutum 3 sun sake rasuwa a jihar Legas
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban ma'aikatan shugaba Buhari, Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya, sanadiyyar kamuwa da cutar Coronavirus da yayi a cikin watan Maris.

A jiya dai an bayyana rahoton cewa mutane 51 sun kamu da cutar ta Coronavirus a Najeriya, inda yawan masu cutar ya karu zuwa 493.

Ya zuwa yanzu an yiwa mutane 159 magani, tuni har an sallamesu daga asibiti ma, inda mutane 17 suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar, kamar dai yadda cibiyar lura da manyan cututtuka ta Najeriya ta ruwaito.

Fadar shugaban kasar ta tabbatar da rasuwar tashi, bayan wani rahoto da mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa Mr Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Fadar shugaban kasa za ta bayyana rasuwar shugaban ma'aikata na Najeriya, Malam Abba Kyari. Marigayin dai ya kamu da cutar ta Coronavirus, kuma yana karbar magani a asibiti, inda a jiya Juma'a 17 ga watan Afrilu Allah yayi masa rasuwa.

"Allah ya yi masa rahama. Zamu bayyana yadda za'ayi jana'izarsa nan ba da dadewa ba," cewar Femi Adesina a sanarwar da ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel