Kwamishinan Ganduje ya yi magana mai harshen damo a kan mutuwar Abba Kyari

Kwamishinan Ganduje ya yi magana mai harshen damo a kan mutuwar Abba Kyari

Kwamishinan Ayyuka da Gine–Gine na jihar Kano, Muaz Magaji ya yi martani a kan rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari inda ya ce yanzu Najeriya ta samu yanci.

An rantsar da Magaji a matsayin kwamishina ne a ranar 5 ga watan Nuwamban 2O19 ya yi wannan martanin ne a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Asabar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A baya kwamishinan ya taba wallafa wani rubutu inda ya yi fatan kada Abba Kyari da dawo ya cigaba da ayyukansa a matsayin shugaban maaikatan fadar shugaban kasa bayan ya kamu da Covid-19 makonni kadan da suka gabata.

Kwamishinan Ganduje ya yi magana mai harshen damo a kan mutuwar Abba Kyari

Kwamishinan Ganduje ya yi magana mai harshen damo a kan mutuwar Abba Kyari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

Kwamishinan ya yi kwarin suna wurin yin maganganu a kan alamura da suka shafi abokan adawarsa a siyasa a shafukan sada zumunta wadda hakan ke jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumuntar.

A daya daga cikin rubuce rubucen da ya wallafa a Facebook, Mista Magaji ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin amma ya kuma ce, "Nasara Nasara ... Najeriya ta samu yanci kuma Abba Kyari ya mutu a cikin annoba ... Mutuwar shahada in har da Imani mutum ya cika!"

A wani sako daban da ya wallafa a dandalin sada zumuntar ya ce, "Ba za ka iya canja tarihi ba ... Ba abinda zai canja ka, halayen ka sune za su nuna wa duniya ko kai waye ... ko kana raye ko kuma ka mutu!"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel