Abba Kyari: Zulum ya tara malamai an yi adduo'i na musamman (Hotuna)

Abba Kyari: Zulum ya tara malamai an yi adduo'i na musamman (Hotuna)

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Asabar ya tara malamai da mutanen da ke sansanin gudun hijira dabandaban a karamar hukuma Ngala domin yi wa marigayi Abba Kyari addua.

Marigayin da ya rasu a jihar Legas bayan ya kamu da cutar coronavirus dan asalin jihar Borno ne.

Labarin rasuwar Abba Kyari da riski Zulum ne a garin Gamboru da ke karamar hukumar Ngala inda ya kwana yana saka idanu kan yadda ake rabon kayan tallafi a sansanin yan gudun hijiran.

Gwamnan ya bar Maiduguri a ranar Jumaa ne zuwa garin na Ngala.

DUBA WANNAN: COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

Bisa umurnin Zulum, babban limamin garin Ngala, Goni Awari Goni Kadiri ya jagoranci sauran limaman garin domin yi wa marigayin addua kamar yadda kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau ya ruwaito.

Gwamnan ya bayar da irin wannan umurnin a sauran sansanin yan gudun hijira a garuruwan Ngala da Gamboru a lokacin da ya ziyarci yan gudun hijiran.

Zulum ya kuma soke ziyarar aiki na kwanaki uku da ya shirya yi.

"Sakamakon rasuwar Alhaji Abba Kyari, Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da ziyarar aikin kwanaki uku da ya yi shirin yi a karamar hukumar Ngala domin rabon kayan abinci da dasa ginin wasu ayyuka," in ji Gusau.

Har wa yau, Zulum ya kuma ziyarci sansanin yan gudun hijira na Ngala inda aka yi gobara a kwanakin baya domin yi musu jaje.

Gwamnan ya yi nazarin irin asarar da aka yi kuma ya bukaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta dauki matakin tallafa musu da kare afkuwar haka a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel