Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja

Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja

- Abba Kyari, marigayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, an birne shi a Abuja

- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan ya kasance a killace tun bayan da aka tabbatar da cewa ya kamu da cutar a watan Maris

- Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, na daya daga cikin wadanda suka karrama marigayin ta hanyar halartar jana'izarsa

Abba Kyari, marigayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, an birne shi a Abuja.

A ranar Juma'a, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da mutuwar Kyari sakamakon cutar coronavirus.

Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Asali: Twitter

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan ya kasance a killace tun bayan da aka tabbatar da cewa ya kamu da cutar a watan Maris.

An birne marigayin ne a makabartar Gudu dake Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, na daya daga cikin wadanda suka karrama marigayin ta hanyar halartar jana'izarsa.

A wata wallafa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi a shafinsa na twitter, ya ce za a birne Kyari ne kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

Abba Kyari ya zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a watan Augustan 2015.

A wannan matsayin da Kyari ya taka, yana da ruwa da tsaki a kan komai da ya shafi shugaban kasar.

Shi yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar sannan yana ganawa da a kalla mutum 20 a kowacce rana.

Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Asali: Twitter

Kamar yadda wani dan jarida da ke aiki a fadar shugaban kasa ya bayyana, a kalla ya kan gana da shugaban kasa sau hudu a rana.

Hakazalika, yana ganawa da gwamnoni da ministoci tare da sauran manyan jami'an gwamnati masu bukatar ganawa da shugaban kasar.

Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Yanzu-yanzu: An birne marigayi Abba Kyari a Abuja
Asali: Twitter

Sakamakon wannan mukamin nashi, mutane da yawa na zarginsa da juya akalar gwamnatin kasar nan, lamarin da shugaban kasar ya musanta.

Abba Kyari ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng