Yanzu-yanzu: An fara sallar jana'izar Abba Kyari a Abuja

Yanzu-yanzu: An fara sallar jana'izar Abba Kyari a Abuja

A yau Asabar 18 ga watan Afirilu ake yin janaizar Malam Abba Kyari, tsohon shugaban maaikatan fadar shugaba Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja.

Mai taimakawa shugaban kasa a fanin kafafen watsa labarai na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a safiyar yau.

Ya ce, "Za a birne Abba Kyari a yau a Abuja bisa tsarin koyarwar addinin musulunci."

Sahara Reporters ta gano cewa za a yi wa marigayi Abba Kyari salla ne a Defence House sanan a birne shi a makabartar Gudu da ke Abuja.

Yanzu-yanzu: An fara sallar jana'izar Abba Kyari a Abuja
Yanzu-yanzu: An fara sallar jana'izar Abba Kyari a Abuja
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Hanyoyi 4 da gwamnati za ta iya isar da tallafi ga talaka cikin sauki

Ministan Sadarwa na Najeriya Sheikh Aliyu Pantami ne ya jagoranci sallar janaizar marigayin a Abuja kamar yadda hotunan da NTA ta wallafa suka nuna.

Daga cikin wadanda suka hallarci sallar janaizar har da mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu.

Shehu ya ce za a gudanar da jana'izar marigayi Kyari ta hanyar bin dokokin da Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, da Ma'aikatar Lafiya ta Kasa suka gindaya.

Har wa yau, ya bayyana cewa za a yi jana'izar ne cikin sirri kuma ba za ayi zaman makoki ba.

Abba Kyari ya rasu ne a ranar Jumaa sakamakon kamuwa da kwayar cutar coronavirus da ya yi jinya.

"Ba za ayi zaman makoki ba da karbar gaisuwa. Ana shawartar iyalai, yan uwa da abokan arziki su yi wa mammacin addu'ar samun gafarar ubangiji," in ji Shehu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel