Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

- Wata sanarwa da muke samu a yanzun nan ta bayyana cewa Allah ya yiwa shugaban ma'aikata Abba Kyari rasuwa

- Babban makusancin ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu ne a jiya Juma'a 17 ga watan Maris bayan kamuwa da cutar Coronavirus

- Mai bawa shugaban kasa shawara a fannin sadarwa Mr Femi Adesina, shine ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, inda yace za ayi jana'izarsa nan ba da dadewa ba

Shugaban ma'aikatan shugaba Buhari, Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya, sanadiyyar kamuwa da cutar Coronavirus da yayi a cikin watan Maris.

A jiya dai an bayyana rahoton cewa mutane 51 sun kamu da cutar ta Coronavirus a Najeriya, inda yawan masu cutar ya karu zuwa 493.

Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya
Source: Twitter

Ya zuwa yanzu an yiwa mutane 159 magani, tuni har an sallamesu daga asibiti ma, inda mutane 17 suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar, kamar dai yadda cibiyar lura da manyan cututtuka ta Najeriya ta ruwaito.

Fadar shugaban kasar ta tabbatar da rasuwar tashi, bayan wani rahoto da mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa Mr Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya

"Fadar shugaban kasa za ta bayyana rasuwar shugaban ma'aikata na Najeriya, Malam Abba Kyari. Marigayin dai ya kamu da cutar ta Coronavirus, kuma yana karbar magani a asibiti, inda a jiya Juma'a 17 ga watan Afrilu Allah yayi masa rasuwa.

"Allah ya yi masa rahama. Zamu bayyana yadda za'ayi jana'izarsa nan ba da dadewa ba," cewar Femi Adesina a sanarwar da ya wallafa.

Labarin yadda ya kamu da cutar ta Coronavirus dai ya fito ne a watan Maris, inda bayan kamuwarshi da cutar, shi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari aka yi masa gwaji ba a samu cutar a jikinshi ba.

Shugaba Buhari, Yemi Osinbajo, gwamnoni da ministoci da dama sun hadu da shi kafin a gabatar da gwajin cutar a jikinshi.

Kyari wanda ya dawo Najeriya daga wata tafiya da yayi zuwa kasar Jamus, a ranar 14 ga watan Maris, ya gana da manyan mutane na Najeriya da dama.

Abba Kyari daga baya ya fito ya bayyana cewa za a kai shi birnin Legas daga Abuja domin ya cigaba da karbar magani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel