Manyan annoba 6 da aka taba yi a duniya da adadin mutanen da kowacce ta hallaka

Manyan annoba 6 da aka taba yi a duniya da adadin mutanen da kowacce ta hallaka

An dade ba a samu barkewar wata annoba ba a duniya kafin zuwan annobar cutar covid-19, wacce ta samo asali daga wani gari mai suna Wuhan a kasar China.

Tarihi ya nuna cewa a baya an samu anobar cututtuka daban-daban da su ka yi sanadiyar mutuwar miliyoyi da dubu daruruwan mutane a mabanbantan lokuta.

1. Kanjamau (HIV/AIDS)

Kwayar cutar kanjamau, wacce aka fara ganowa a kasar Congo a shekarar 1976, ta shiga cikin tarihin manyan annoba idan ana maganar cututtuka ma su yaduwa da su ka kashe dumbin jama'a.

Wani kiyasin masana ya bayyana cewa cutar HIV ta kashe mutane fiye da miliyan talatin da shidda (36m) daga shekarar 1981 zuwa shekarar 2012.

Duk da har yanzu akwai cutar kanjamau, tasirin da magunguna ke yi a kan kwayar cutar tare da gano hanyoyin kare kai daga kamuwa da ita ya rage mata kwarjini.

2. Annobar mura (1968)

An fara samun bullar annobar wata cutar mura da ake kira 'Hong Kong Flu' a garin Hing Kong na kasar China a shekarar 1968.

Cikin kwanaki bakwai kacal kwayar cutar ta bulla kasar Singapore da Vietnam kafin ta bulla kasar Philippines, India, Australia, Turai da Amurka a cikin wata uku.

Cutar ta kashe mazauna Hong Kong 500,000; kaso 15% na jama'ar garin, a 1968, sannan ta yi sanadin mutuwar fiye da miliyan daya a duniya.

3. Annobar cutar mura ta nahiyar Asia (1956-1958)

Wannan annoba ta samo asaline daga kasar China a shekarar 1956, sannan ta kai har zuwa shekarar 1958.

A shekaru biyu da annobar ta yi, ta yadu zuwa yankin Guizhou, kasar Singapore da Amurka.

Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ce ta kawo karshen jayayyar da ake yi a kan adadin mutanen da annobar ta kashe bayan ta bayyana cewa annobar ta kashe a kalla mutane miliyan biyu a fadin duniya.

4. Annobar cutar mura (1918)

An samu bullar annobar wata cutar mura da ta firgita duniya a tsakanin shekarar 1918 zuwa 1920.

Annobar ta kasane daya daga cikin wadadnda su ka kashe dumbin mutane a cikin kankanin lokaci bayan ta hallaka mutane miliyan 20 zuwa 50.

Duk da an sha samun barkewar annobar mura a duniya, ita wannan annoba ta sha banban da sauran saboda adadi da yanayin mutanen da ta kashe.

A cikin sati 25 da barkewar annobar, ta kashe a kalla mutane miliyan 25, yawancinsu matasa ma su koshin lafiya, majiya karfi a jikinsu, yayin da ta kyale dattijai da kananan yara da garkuwar jikinsu ke da rauni.

5. Annobar cutar kwalera karo na shidda (1910-1911)

Kamar sauran annobar cutar kwalera da aka yi kafin zuwanta, ita ma ta samo asaline daga kasar Indiya inda ta kashe mutane fiye da 800,000 kafin ta yadu zuwa nahiyar Afrika da Rasha.

Daga wannan annoba ne kasar Amurka ta koyi darasi, yayin da ta yi gaggawa ta kebe wadanda su ka kamu, lamarin da ya takaita adadin mutanen da annobar ta kashe zuwa 11.

An samu raguwar annobar cutar kwalera daga shekarar 1923, amma har yanzu a kan samu barkewarta a kasar Indiya lokaci zuwa lokaci.

6. Bakar mutuwa (1346-1353)

Daga shekarar 1346 zuwa 1353, an samu barkewar annobar wata cuta mai suna 'bubonic plague' wacce ta kashe mutane 75 zuwa 200 a nahiyar Asia, Turi da Afrika.

Ana zargin cewa kwayar cutar, wacce ta samo asali daga nahiyar Asia, ta yadu zuwa nahiyar Turai da Afrika ta berayen da ke shiga kayan da ake dora wa jirgin ruwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel