Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk

Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk

Sanata Ali Ndume ya tsaya kai da fata a kan bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige shugabar kwamitin raba kayan tallafin Coronavirus, Minista Sadya Umar Farouk.

Ndume ya bayyana haka ne biyo bayan wata zazzafar martani da fadar shugaban kasa ta mayar masa bayan ya yi zargin mutanen dake zagaye da shugaba Buhari marasa gaskiya ne.

KU KARANTA: Zargin barayi ne a zagaye da Buhari: Fadar shugaban kasa ta mayar da biki ga Ndume

The Nation ta ruwaito Ndume ya bayyana haka ne a Borno yayin da yake yaba ma Buhari bisa tallafin da yake baiwa yan Najeriya sakamakon halin da suke ciki saboda annobar Coronavirus.

Sai dai a jawabin nasa, ya koka game da hadiman Buharin, wanda yace suna amfani da damarsu suna cutar da yan Najeriya har ma suna kashe yan Najeriya.

Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk

Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk
Source: Twitter

Da wannan ne Sanatan ya nemi Buhari ya rusa kwamitin rabon tallafi dake karkashin ministar kula da walwal, Sadiya Umar Farouk domin a yi ma jama’a adalci.

Sai dai, Kakaakin shugaban kasa, Garba Shehu ya mayar da martani a madadin fadar gwamnatin, inda ya nemi Ndume ya kira sunan marasa gaskiyan dake tare da Buhari .

“Da aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 2015, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace shi na kowa ne, kuma ba nakowa ba, kuma har yanzu hakan take. Ya yarda da yi ma jama’a hidima, kuma yake son ganin hadimansa suna yi.

“Idan har an samu wani da ba shi da gaskiya a tare da shi, ya kamata a bayyana shi, amma fa a tabbata akwai kwakkwarar hujja dake nuni ga haka, ba karairayi ba, don haka idan har dan siyasan nan yana da hujja, toh ya bayyana sunan wanda yake zargi da laifinsa.

“Don haka, kawai don wani dan siyasa mara godiyan Allah ya tara yan jaridu ya yi musu jawabi ba zai taba zama hujj ba.” Inji shi.

Sai dai a wata hira da Ndume yayi da The Nation ta wayar tarho, ya bayyana cewa shi dai ya riga ya fadi ra’ayinsa, kuma yana nan a kan bakarsa, don haka ba zai yi cacar baki da wani ba.

“Ba ni da lokacin musayar yawu da wani a kan maganan da nayi game da rabon kayan tallafi bayan na samu bayanai na kai tsaya daga wajen talakawa a matsayina na mutumin talakawa, don haka na fadi nawa, kuma na tsaya a kai.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel