Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sallami masu Corona 3, El-Rufa'i da mutum 1 suka rage

Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sallami masu Corona 3, El-Rufa'i da mutum 1 suka rage

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sallamar masu cutar Coronavirus uku dake jinya a jihar bayan an tabbatar da cewa sun samu sauki kuma sun barranta daga cutar.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed-Baloni ta alanta hakan ne a jawabin da ta saki da yammacin Juma'a, 17 ga watan Afrilu, 2020.

Jawabin yace: "Ma'aikatar lafiyan jihar Kaduna tana mai sanar da sallamar marasa lafiya uku bayan sun warke daga COVID-19."

"Mutane uku da aka saki na cikin mutane shida da suka kamu da cutar a jihar."

"Gwaji biyu da aka yi musu sun nuna cewa sun tsira daga cutar kuma yanzu an sallamesu."

"Hakan ya kawo adadin wadanda aka sallama a jihar Kaduna cikin makon nan hudu. Mutane biyu kadai suka rage kuma muna kyautata zaton nan ba da dadewa ba za'ayi."

Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sallami masu Corona 3, El-Rufa'i da mutum 1 suka rage

Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sallami masu Corona 3
Source: UGC

KU KARANTA: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu

Dazu mun kawo muku rahoton cewa an samu karin mutane bakwai da suka samu sauki bayan kwashe makonni suna jinya sakamakon cuta mai toshe numfashi data addabi duniya watau COVID-19.

Gwamnatin jihar Enugu ta alanta sallamar mutane biyu tal-in-tal da suka rage a cibiyar killacewarta bayan samun waraka daga cutar Coronavirus.

Mutane biyun da aka sallama mata da miji ne wadanda suka dawo Najeriya daga kasar Ingila kwanakin baya.

Kwamishanan lafiyar jihar yayin sanar da labarin sallamarsu ya yi kira ga al'ummar jihar su dage su bi umurnin gwamnati don hana yaduwar cutar.

A jihar Edo kuwa, gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya sanar da cewa an sallami mutane biyar masu dauke da cutar bayan gwaji ya nuna cewa babu sauran cutar cikin jikinsu.

Obaseki ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 17 ga Afrilu a shafinsa ta Facebook.

Duk a yau, hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja na ci bal-bal yanzu haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel