Yanzu-yanzu: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu

Yanzu-yanzu: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu

- A kalla mutum 6 cikin 'yan kwamitin yaki da Covid-19 a jihar Kano suka kamu da muguwar cutar, majiya mai karfi ta sanar wa jaridar Daily Nigerian

- Majiyar ta ce tuni dai aka kai wadanda suka tabbata dauke da cutar zuwa cibiyar killacewa da ke Kwanar Dawaki da ke wajen birnin Kano don fara karbar magani

- An gano cewa zukatan 'yan kwamitin yaki da cutar na jihar Kano ya matukar girgiza bayan sun gano cewa mataimakin shugaban kwamitin na dauke da cutar

A kalla mutum 6 cikin 'yan kwamitin yaki da Covid-19 a jihar Kano suka kamu da muguwar cutar, majiya mai karfi ta sanar wa jaridar Daily Nigerian.

Majiyar ta ce tuni dai aka kai wadanda suka tabbata dauke da cutar zuwa cibiyar killacewa da ke Kwanar Dawaki da ke wajen birnin Kano don fara karbar magani.

An gano cewa zukatan 'yan kwamitin yaki da cutar na jihar Kano ya matukar girzgiza bayan sun gano cewa mataimakin shugaban kwamitin na dauke da cutar.

Hakan ne kuwa yasa aka dage taron da za su yi daren jiya har sai baba ta gani.

"Mataimakin shugaban kwamitin ya bayyana dauke da cutar tare da wasu likitoci biyu daga cikin 'yan kwamitin," majiyar tace.

Yanzu-yanzu: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu
Yanzu-yanzu: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu

Mutane 26 ne a halin yanzu suke dauke da cutar a jihar Kano ta Najeriya kamar yadda NCDC ta bayyana.

"Da karfe 10:20 na daren 16 ga watan Afirilun 2020, mutum 442 ne ke dauke da cutar a Najeriya. An sallama mutum 152 daga asibiti yayin da mutum 13 suka rasu," NCDC ta bayyana.

Amma kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu bayan an gano cewa sun yi mu'amala da wani mai cutar.

Mambobin kwamitin hana yaduwar cutar COVId-19 din wacce mataimakin gwamna Gawuna ke shugabanta, sun hada da Amina Umar Ganduje, kwamishinan lafiya Aminu Tsanyawa, kwamishinan muhalli Kabiru Getso da Imam Wada, sakataren kwamitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel