COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu

COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu

- Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu

- Sun yanke shawarar killace kansu ne bayan an gano cewa mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Abdulrazaq Garba Habibu na dauke da cutar

- Kamar yadda hukumar kula tare da takaita yaduwar cutuka ta bayyana, da karfe 10:20 na daren Alhamis, an samu mutane 21 a jihar masu dauke da cutar

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, kwamishinoni uku da diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun killace kansu bayan an gano cewa sun yi mu'amala da wani mai cutar.

Mambobin kwamitin hana yaduwar cutar COVId-19 din wacce mataimakin gwamna Gawuna ke shugabanta, sun hada da Amina Umar Ganduje, kwamishinan lafiya Aminu Tsanyawa, kwamishinan muhalli Kabiru Getso da Imam Wada, sakataren kwamitin.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa sun yanke shawarar killace kansu ne bayan an gano cewa mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Abdulrazaq Garba Habibu na dauke da cutar.

Majiya mai karfi daga gwamnatin ta ce, "Kun san tunda tare suke aiki da mataimakin shugaban kwamitin kafin ya san yana dauke da cutar, zai fi idan sauran mambobin suka kullace kansu.

"An diba jininsu don dubawa ko suna dauke da cutar amma har yanzu ba a samu sakamakon ba.

COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu
COVID-19: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Titunan Kano bayan dokar hana zirga-zirga ta fara aiki (Hotuna)

"Muna fatan sakamakon ya nuna basu dauke da cutar. Amma ina tabbatar muku da cewa dukkan 'yan kwamitin suna killace tare da jiran sakamako," majiyar tace.

Idan za mu tuna, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da kwamitin a ranar 21 ga watan Maris 2020.

Alhakin takaita yaduwar annobar a jihar Kano ya hau kansu tare da duk wani kokarin zakulo masu cutar.

Kamar yadda hukumar kula tare da takaita yaduwar cutuka ta bayyana, da karfe 10:20 na daren Alhamis, an samu mutane 21 a jihar masu dauke da cutar.

A yau ne dokar hana zirga-zirga da gwamnan jihar Kano ya saka ta fara aiki.

An ga hotunan birnin Kano kamar an shareshi saboda jama'ar jihar sun yi biyayya ga dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel