Zargin barayi ne a zagaye da Buhari: Fadar shugaban kasa ta mayar da biki ga Ndume

Zargin barayi ne a zagaye da Buhari: Fadar shugaban kasa ta mayar da biki ga Ndume

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani mai zafi ga Sanata Ali Ndume bayan ya zargi yan gaban goshin shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin gaskiya da tafka rashawa.

Ndume ya bayyana haka ne a jahar Borno yayin da yake yaba ma Buhari bisa tallafin da yake baiwa yan Najeriya sakamakon halin da suke ciki saboda annobar Coronavirus.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus a Kano ya kamu da cutar

Sai dai a jawabin nasa, ya koka game da hadiman Buharin, wanda yace suna amfani da damarsu suna cutar da yan Najeriya har ma suna kashe yan Najeriya.

Da wannan ne Sanatan ya nemi Buhari ya rusa kwamitin rabon tallafi dake karkashin ministar kula da walwal, Sadiya Umar Farouk domin a yi ma jama’a adalci.

Zargin barayi ne a zagaye da Buhari: Fadar shugaban kasa ta mayar da biki ga Ndume
Zargin barayi ne a zagaye da Buhari: Fadar shugaban kasa ta mayar da biki ga Ndume
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito Kakaakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya mayar da martani a madadin fadar gwamnatin, inda ya nemi Ndume ya kira suna idan ba tsoro ba.

A cewar Garba, abin takaici ne ka ji wani dan siyasa yana zargin wasu mutane a gwamnatin nan da bai bayyana sunayensu ba da aikata wasu laifuka da bai bayyana ba.

“Da aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 2015, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace shi na kowa ne, kuma ba nakowa ba, kuma har yanzu hakan take. Ya yarda da yi ma jama’a hidima, kuma yake son ganin hadimansa suna yi.

“Shugaban ya sha nanata duk wanda ba shi da wannan manufa irin nasa toh ya kama gabansa, an sallami manyan jami’an gwamnatin nan a lokuta daban daban saboda hakan, haka zalika ya yarda da gaskiya da biyayya.

“Idan har an samu mara gaskiya a tare da shi, toh a bayyana shi, amma fa da kwakkwarar hujja dake nuni ga haka, ba karairayi ba, don haka idan har dan siyasan nan yana da hujja, toh ya bayyana sunan wanda yake zargi da laifinsa.

“Don kawai ka yi zargin kayan tallafin COVID-19 basu isa ba, ba zai taba zama hujja ba, babu inda ake sauya hukumar gwamnati yayin da ake tsaka da annoba ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

“Don haka, kawai don wani dan siyasa mara godiyan Allah ya tara yan jaridu ya yi musu jawabi ba zai taba zama hujj ba.” Inji shi.

Daga karshe Garba ya yi kira ga yan Najeriya su hada kai da gwamnati don kawo karshen annobar Coronavirus ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel