Akwai yiwuwar Afirka za ta zama cibiyar coronavirus - WHO

Akwai yiwuwar Afirka za ta zama cibiyar coronavirus - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi nazari gami da hangen nesa a kan yiwuwar nan gaba Afirka ka iya zama cibiyar cutar coronavirus, wadda ta yiwa duniya kawanya a yanzu.

A makon jiya dai mutanen dake kamuwa da cutar ya kara yawaita a nahiyyar, inda aka samu kimanin mutum 18,000 da cutar ta harba, kuma tuni mutum 1000 sun riga mu gidan gaskiya.

Duk da yawan adadin masu cutar da aka samu a nahiyar, basu kai yawan adadin da Amurka da Turai ke dashi ba a yanzu.

A kiyasin da hukumar ta yi, cutar na yaduwa ne daga manyan birane zuwa wasu yankunan a nahiyar.

Sai dai hukumar ta ce nahiyar ba ta da wadatattun na'urori na taimakon numfashi ga masu dauke da wannan cuta.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya; Tedros Adhanom

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya; Tedros Adhanom
Source: UGC

A yanzu an tabbatar da akalla mutum 19,000 na dauke da wannan cuta, inda aka samu wadanda suka mutu kimanin 970 a nahiyar mai jama'u kimanin biliyan 1.3.

Kasashen da ke yankin Arewacin nahiyyar sun fi fama da wannan mummunar annoba da ta dugunzuma dukkanin kasashe.

Kasashen da su ka fi fama da cutar fiye da sauran sassan kasashen sun hadar da; Algeria, Masar da kuma Morocco.

Kowace daya daga cikin kasashen uku na dauke da adadin masu cutar sama da 2,000 inda akalla kowace kasa mutum 100 tuni sun ce ga garinku nan.

Ita ko kasar Afirka ta kudu na da adadin mutum 2,000 wanda suka harbu da cutar corona inda mutum 48 sun mutu.

Sai kuma nan gida Najeriya wadda tafi kowace kasa yawan al'umma a nahiyyar Afirka, ta samu mutum 442 da suka harbu yayin da tuni mai yankan kauna ta yi gaba da mutane 48.

A bangare guda kuma, Darektan WHO mai kula da nahiyyar Afirka, Dr Matshidido Moeti, ta bayyana hasashenta kan dalilin da ya hana cutar yin mummunan tasiri a nahiyyar.

KARANTA KUMA: June Almeida: Matar da ta fara gano kwayar cutar corona a duniya

Dr Moeti ta ce akwai yiwuwar rashin tafiye-tafiye daga wata kasa zuwa wata ya taka rawar gani wajen hana yaduwar cutar a nahiyyar idan an kwatanta da nahiyyar Turai da kuma Amurka.

Ta ke cewa, "Idan ku ka kalli yawan mutanen da suka yi balaguro, Afirka na da karancin mutanen da suke yin tafiye-tafiye."

A cewar ta, cutar tana ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a Afirka sakamakon ci gaba da yadda a kullum mutanen da ke kamuwa da ita ke karuwa.

Yanzu haka dai ta ce cutar tana yaduwa a manyan biranen kasashe irin su Najeriya, Afirka ta Kudu, Ivory coast, Kamaru da kuma Ghana.

Har ila yau akwai wasu kasashe 15 a nahiyyar da cutar ba ta yadu da yawa ba kuma akwai yiwuwar muddin aka ci gaba da tafiya a hakan, kasashen za su iya shawo kan cutar ta hanyar daukar matakan bayar da tazara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel